Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Yi Fatali da Kudin Fansa, Sun Fadi Dalilin Raina Naira Miliyan 3
- Mazauna kauyen Gidan-Goga a Zamfara sun koka game da yadda miyagun 'yan bindiga su ka ki karbar kudin fansa da aka ba su
- Wani magidanci a yankin, Abubakar Shehu ya bayyana cewa an sace 'ya'yansa mata uku a cikin mutane 26 da aka yi garkuwa da su
- Mazaunan sun fadi yadda hukumomi su ka yi biris da su duk da cewa an sanar da su wurin da 'yan ta'addan ke zauna a kusa da kauyen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara - Mutanen Zamfara sun shiga mawuyacin hali bayan ‘yan bindiga sun ki amincewa da kudin da aka tattara domin sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.
Miyagun ‘yan ta’addan sun ki karɓar N3m da aka bayar a matsayin kuɗin fansa don sakin mutum 26 da aka sace daga kauyen Gidan-Goga, ƙaramar hukumar Maradun.
A wani labari da ya kebanta ga Punch, akwai magidancin da aka sace masa ‘ya’yansa mata guda uku, kuma yanzu ya rasa inda za isa hankalinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mazauna Zamfara sun fada mawuyacin hali
Wani ɗan asalin kauyen, Abubakar Shehu, wanda ‘ya’yansa mata uku na daga cikin waɗanda aka sace, ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun sace mutane 26 a harin da su ka kai masu.
Shehu ya bayyana cewa wadanda aka sace sun haɗa da mata 19 da maza shida, inda ɗaya daga cikin ‘ya ’yansa ke shirin aure kafin sace ta.
"An yi watsi da mu,” Mutanen Zamfara
Al’ummar, Gidan-Goga, wadda ke fuskantar hare-hare daga ‘yan bindigasun ce mugayen mutanen na aiki daga wani sansani kusa da kauyen.
Mazauna kauyen sun ƙara da cewa duk da sanar da hukumomin tsaro na yankin game da lamarin, ba a ɗauki wani mataki ba.
Abubakar Shehu ya ce;
“Mun sanar da jami’an tsaro na ƙaramar hukuma, amma ba a yi komai ba don magance lamarin. Wannan ba shi ne karo na farko da aka kai wa kauyenmu hari ba,”
Zamfara: Sojoji sun fatattaki 'yan ta'adda
A wani labarin, kun ji cewa zaratan dakarun sojojin Najeriya sun ragargaza miyagun 'yan ta'addan da ke fakewa a sassan Zamfara bayan sun kai hari maboyar bata-garin mutanen.
A harin da aka yi nasarar hallaka 'yan ta'adda da dama, jami'an sojojin sun kwato babura yayin da sauran miyagun 'yan bindigar su ka tsere a kokarinsu na tsira daga wutar dakarun.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng