Diyar Ado Bayero Ta Sake Neman Taimakon Al'umma, Ta Roki Tinubu da Abba Kabir

Diyar Ado Bayero Ta Sake Neman Taimakon Al'umma, Ta Roki Tinubu da Abba Kabir

  • 'Yar marigayi sarkin Kano, Ado Bayero ta sake tura kokon bara ga Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Zainab Ado Bayero ta ce har yanzu suna cikin mummunan yanayi kamar yadda ta sha fada a baya a jihar Lagos
  • Gimbiyar ta ce abin takaici ne yadda ake cin zalinsu kuma musamman daga masarautar Kano

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Diyar marigayi tsohon sarkin Kano, Ado Bayero ta sake fitowa inda ta nemi taimako kan halin da suke ciki.

Zainab Ado Bayero ta bayyana cewa dan uwanta, Ahmed Tijjani Ado Bayero da mahaifiyarta suna cikin halin takura a birnin Lagos a ranar 8 ga Disambar 2024.

Zainab Ado Bayero ta sake rokon al'umma alfarma
Diyar Ado Bayero ta nemi alfarma daga Bola Tinubu da Abba Kabir. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Sanusi Lamido Sanusi.
Source: Twitter

Zainab Ado Bayero ta sake neman taimako

Vanguard ta ce gimbiyar ta bayyana kanta a matsayin “marubuciya mai kishin mata da ‘yancinsu inda ta sake yin kira ga al’umma don neman taimako.

Kara karanta wannan

"Za ku iya rasa rawaninku," Sarki Sanusi II ya fadi abin da ke barazana ga sarakai a Kano

Zainab Ado Bayero ta roki Bola Tinubu domin kawo mata dauki yadda aka ci mutuncinsu a Kano musamman daga masarauta.

Har ila yau, Zainab ta sake tura kokon bara ga Abba Kabir na jihar Kano da ya yi amfani da ikonsa a matsayin gwamna don kawo karshen matsalar da suke ciki.

'Yar Ado Bayero ta roki Tinubu da Abba Kabir

“A matsayina na mace kuma ‘yar kasa, ina tambayar Shugaba Bola Ahmed Tinubu shin daidai ne a ci zalina ta hannun wasu daga cikin masarautar Kano?
"Wadannan da ake gani a matsayin masu kula da masarautar Kano suna karbe ‘yancina da dan uwana da kuma na mahaifiyata."
“Ina kuma rokon gwamnan jihar Kano, wanda shi ma dan uwa ne kuma uba ga mutanen Kano, da ya kawo karshen wannan wahala."

- Zainab Ado Bayero

Zainab Ado Bayero ta nemi taimakon gwamnati

Kun ji cewa yar gidan Sarkin Kano, marigayi Ado Bayero ta yi bayani bayan da ta sha suka kan fitowa tana neman taimako daga gwamnati karo na biyu.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da malamin addini ya bata, an bukaci addu'o'i

Zainab Ado Bayero ta bayyana cewa sun dade da shiga cikin mummunan yanayi amma mutane sun gaza fahimtar halin da suke ciki.

Ta kuma fadi abin da yasa suke neman taimako a wajen al'ummar Najeriya maimakon komawa zuwa gida Kano wajen yan uwanta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.