"Abin da na Faɗawa Tinubu kan Matsalar Tsaron Najeriya," Sabon Hafsan Soji Ya Magantu

"Abin da na Faɗawa Tinubu kan Matsalar Tsaron Najeriya," Sabon Hafsan Soji Ya Magantu

  • Hafsan rundunar sojin kasar Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya ziyarci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a Aso Villa
  • Oluyede ya ce ya tabbatarwa da Shugaba Tinubu cewa zai zai kawo karshen matsalar tsaron da aka kwashe shekaru ana fama da ita
  • Sabon shugaban sojojin ya ce a kwanakin baya ya ziyarci rundunonin sojoji a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sabon hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ce ya bai wa shugaban ƙasa, Bola Tinubu tabbacin cewa zai magance matsalar tsaron Najeriya.

Janar Oluyede ya ce ƙungiyar ƴan ta'addan Lakurawa da sauran kungiyoyin ta'addanci za su zama tarihin nan ba da daɗewa ba.

Tinubu da Oluyede.
Sabon hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Oluyede ya gana da Tinubu Hoto: @HWNigeriaArmy
Asali: Twitter

Olufemi Oluyede ya faɗi hakan ne da yake zantawa da manema labara a fadar gwamnati jim kaɗan bayan ganawa da Shugaba Tinubu yau Litinin, Vanguard tv ta kawo.

Kara karanta wannan

Daga fara aiki, hafsan sojojin Najeriya ya fadi lokacin kawo karshen 'yan Lakurawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da sabon hafsan sojin ya faɗawa Tinubu

Dangane da abin da ya tattauna da Tinubu a ziyarar, Oluyede ya ce:

“Tana da alaƙa da naɗina, na zo nan ne domin in tabbatar wa shugaban kasa cewa zan yi iya kokarina wajen ganin Najeriya ta inganta ta fuskar tsaro. Kuma da yiwuwar zan bi wata hanya daban."
"Zan shige gaba har mu yi nasara ta yadda tsaron Najeriya zai inganta, wannan shi ne babban burin da na sa a gaba. Kuma na zo na nemi goyon bayan shugaban ƙasa."

Shugaban sojoji zai sa kafar wando daya da miyagu

Sabon hafsan sojin ya kuma yi magana a kan ziyarar da ya kai sansanonin sojoji a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.

Oluyede ya ce ya kai waɗannan ziyarori ne domin tattaunawa ds sojoji, da kuma fahimtar da su cewa akwai bukatar a kawo karshen wadannan matsalolin na tsaro.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga uku, sabon hafsan rundunar sojojin Najeriya ya kama aiki

Ya jaddada masu cewa daga yau ina bukatar ganin sakamako mai kyau yaƙin da suke yi da ƴan tada ƙayar baya, rahoton Channels tv.

Sabon hafsan soji ya shirye murkushe 'yan bindiga

A wani rahoton, an ji cewa hafsan sojojin ƙasa, Janar Oluyede ya jaddada cewa nan ba da jimawa da ƴan ta'addan Lakurawa za su zama tarihi.

Ya ce Najeriya da wasu ƙasashen maƙwabta sun fara haɗa kai domin murkushe ƴan ta'addan waɗanda suka tare a Arewa maso Yamma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262