Sojoji, 'Yan Sanda da 'Yan Banga Sun Hadu Sun Gwabza da Tulin 'Yan Bindiga

Sojoji, 'Yan Sanda da 'Yan Banga Sun Hadu Sun Gwabza da Tulin 'Yan Bindiga

  • Rundunar ’yan sanda a jihar Kebbi ta sanar da ceto mutane 36 daga hannun masu garkuwa da mutane a yankunan Danko da Wasagu
  • Tawagar haɗin gwiwa ta ’yan sanda, sojoji, da 'yan banga sun yi nasarar fatattakar ’yan bindigar tare da ceto mutane da dama
  • Kwamishinan ’yan sanda, Bello M. Sani, ya yabawa jami’an tsaro tare da yin kira ga ci gaba da haɗin kai wajen yaki da 'yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Rundunar ’yan sanda ta jihar Kebbi ta sanar da nasarar ceto mutum 36 da aka sace a ranar 8 ga Disamba, 2024, a yankin Danko/Wasagu.

Mutanen sun fada hannun masu garkuwa ne yayin da suke dawowa daga gonakinsu a kan hanyar Mairairai/Bena.

Kara karanta wannan

Shugaban masu garkuwa da mutane, Idris Alhaji Jaoji ya shiga hannu

Yan sanda
'Yan sanda sun ceto mutane 36 a Kebbi. Hoto: Nigerian police Force
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Bello M. Sani, ya ce nasarar ta zo ne sakamakon haɗin gwiwa tsakanin ’yan sanda, sojoji, da 'yan banga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka ceto mutane 36 a Kebbi

An ruwaito cewa wani gungun ’yan bindiga sun tare hanya tare da sace mutum 36 da ke dawowa daga gonakinsu a jihar Kebbi.

Rahoton Vanguard ya nuna cewa bayan satar, jami'an tsaro sun hadu, sun yi wa ’yan bindigar kwanton bauna inda suka yi musayar wuta.

Bayan musayar wutar, jami’an tsaro sun rinjayi ’yan bindigar, wanda hakan ya sa suka tsere cikin daji tare da raunukan harbin bindiga kuma an ceto dukkan mutanen da suka sace.

An jinjinawa jami'an tsaro a Kebbi

Kwamishinan ’yan sanda na jihar Kebbi, CP Bello M. Sani, ya bayyana gamsuwarsa da jajircewar jami’an tsaron da suka kai farmakin.

CP Bello M. Sani ya ce nasarar ta nuna kwarewa da sadaukarwar jami’an tsaro a kokarinsu na tabbatar da tsaro a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza kazamin fada da 'yan bindiga, an kwato motar 'yan ta'adda

Haka kuma, Bello ya yi kira ga jami’an tsaro da su kara kaimi wajen haɗin kai tsakanin su da sauran bangarorin tsaro don tabbatar da cewa jihar Kebbi ba ta zama mafakar masu aikata laifi ba.

An tarwatsa 'yan bindiga a jihohi

A wani rahoton, kun ji cewa ‘yan sanda sun ceto mutanen da aka sace a Katsina, Akwa Ibom, Rivers, da Taraba.

Haka zalika 'yan sanda sun samu nasarar kwato makamai da dama, ciki har da bindiga kirar AK-47, rigar kariya daga harsasai da kayan sojoji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng