'Yan Bindiga Sun Shiga Uku, Sabon Hafsan Rundunar Sojojin Najeriya Ya Kama Aiki

'Yan Bindiga Sun Shiga Uku, Sabon Hafsan Rundunar Sojojin Najeriya Ya Kama Aiki

  • Hafsan rundunar sojojin Najeriya Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya kama aiki a hukumance yau Litinin, 9 ga watan Disamba
  • Dakarun sojoji sun yi ɗan karamin biki da faretin ban girma gabanin sabon shugabansu ya shiga ofis a hedkwatar sojoji da ke Abuja
  • Shugaba Tinubu ya naɗa Janar Oluyede a matsayin hafsan soji na 24 bayan mutuwar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja a Nuwamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Laftajanar Janar Olufemi Oluyede ya kama aiki a matsayin hafsan rundunar sojin kasa ta Najeriya (COAS) na 24 a tarihi.

Dakarun sojoji sun yi ɗan karamin biki da faretin girmamawa yayin da hafsan sojin ya shiga ofis yau Litinin, 9 ga watan Disamba a hedkwatar sojoji da ke Abuja.

Hafsan sojoji, Janar Oluyede.
Hafsan rundunar sojin ƙasa, Janar Oluyede ya kama aiki Hoto: @HQNigeriaArmy
Asali: Twitter

Hakan na kunshe a wata sanarwa da rundunar sojojin ta wallafa shafinta na manhajar X watau Tuwita.

Kara karanta wannan

Najeriya da kasashen waje sun fara luguden wuta domin murkushe Lakurawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Naɗin sabon hafsan rundunar sojojin ƙasa

Shugaba Bola Tinubu ya nada Oluyede a matsayin mukaddashin hafsan soji sakamakon rashin lafiyar Laftanar Taoreed Lagbaja, wanda ya rasu daga baya.

Kafin nadin nasa, Janar Oluyede ya rike mukamin kwamandan runduna ta 56 ta hukumar sojojin Najeriya da ke Jaji, Kaduna.

Oluyede mai shekaru 56 da marigayi Lagbaja sun zauna a aji ɗaya kuma suna daga cikin rukunin ɗalibai na 39 da aka yaye a kwalejin sojoji da ke Kaduna.

Sabon hafsan sojoji ya kama aiki

Da yake jawabi yayin da ya kama aiki a hukumance, sabon hafsan sojojin ya jaddada kudirinsa na jawo kowa a jiki wajen tafiyar da shugabancin rundunar soji.

Ya yabawa hafsoshi da sojoji bisa goyon baya da jajircewa da suka nuna a lokacin bukukuwan jana’izar marigayi COAS, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

Janar Oludyede ya nanata muhimmancin lalubo sababbin hanyoyi da dabaru domin kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Kudirin haraji da abubuwa 9 da suka yi wa gwamnatin Tinubu illa a Arewacin Najeriya

Janar Musa ta faɗi hanyar dawo da tsaro

Kun ji cewa hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya bayyana cewa ƙarfin soji kaɗai ba zai magance matsalar tsaron ƙasar nan ba.

Janar Musa ya ce bayan amfani da ƙarfin soji, akwai hanyoyin da ya kamata a bi kafin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262