"Za Ku Iya Rasa Rawaninku," Sarki Sanusi II Ya Fadi Abin da ke Barazana ga Sarakai a Kano

"Za Ku Iya Rasa Rawaninku," Sarki Sanusi II Ya Fadi Abin da ke Barazana ga Sarakai a Kano

  • Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bayyana yadda bincike ya nuna yawan kararrakin cin zarafi a kotuna
  • Sanusi II ya bayyana cewa masarauta ba za ta lamunci duk wani basarake da ke lakadawa matarsa duka ba
  • Sarkin ya shawarci gwamnati kan yi wa wasu sassan kunjdin 'penal code' gyara don dakile cin zarafin mata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Sarkin Kano 16, Malam Muhammadu Sanusi II ya gargaɗi masu riƙe da sarautun gargajiya da su guji abin da zai raba su da rawaninsu.

Muhammadd Sanusi II ya bayyana cewa duk basaraken da masarauta ta samu labarin ya na bugun matarsa, to ya yi bankwana da rawanin da aka naɗa masa.

Sarki
Sarki Sanusi ya ja kunnen masu dukan matansu Hoto: @masarautarkano
Asali: Twitter

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa Sarkin Kano ya yi gargadin yayin bude taron kasa na 2024 kan rawar ra'ayin jagororin musulunci wajen dakile cin zarafin mata.

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito kan 'dalilin' mamaye fadar Sanusi II, an ce hakan ka iya zama alheri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa ta kan shawarci 'ya'yansa da cewa duk wacce mijinta ta mare ta, ta sa hannu ta rama, domin babu dalilin cin zarafi a gidan aure.

Sarki Sanusi II ya nemi a gyara sashen 'penal code'

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya nemi a yi kwaskwarima ga sashen kundin 'penal code',wanda ya ba magidanci damar ya ladabtar da matarsa.

Daily Trust ta ruwaito Sarkin ya bayyana cewa sashen na buƙatar gyara ganin yadda wasu magidantan ke wuce gona da iri wajen dogaro da ɓangaren wajen cin zarafin matansu.

Sarkin Kano ya fusata da cin zarafin mata

Tsohon gwamnan babban bankin kasar nan kuma Sarki a Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya ce bincike ya bankado yadda 45% na koke a kotu, cin zarafi ne.

Ya nanata cewa koyarwar addinin musulunci ya haramta cin zarafin mata, inda ya buƙaci gwamnati ta mayar da cin zarafin a gidan aure babban laifi.

Kara karanta wannan

Ana jimamin rasa rayuka a Zamfara, ana zargin 'bam' ya tarwatse da wani a Niger

Gwamnati ta fusata da kewaye fadar Sarkin Kano

A baya, kun ji cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bayyana matuƙar takaici a kan yadda aka samu jami'an tsaro, musamman ƴan sanda su ka kewaye fadar Sarkin Kano.

An wayi gari da ganin jami'an tsaro da motocin yaƙi sun tare kofar fita daga Fadar Muhammadu Sanusi duk da ya daura aniyar raka hakimin Bichi fadarsa a ranar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.