'Yan Sanda Sun Kai Dauki, Sun Ceto Mutanen da 'Yan Bindiga Suka Sace

'Yan Sanda Sun Kai Dauki, Sun Ceto Mutanen da 'Yan Bindiga Suka Sace

  • Shirin ƴan bindiga na yin garkuwa da wasu mutane ya samu cikas a jihar Taraba a Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Jami'an ƴan sanda sun bi bayan ƴan bindigan bayan sun yi garkuwa da wasu mutane a ƙauyen Sibre
  • Ƴan sanda tare da haɗin gwiwar ƴan banga sun yi artabu da ƴan bindigan inda suka kore su tare da ceto mutanen da suka sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Jami'an rundunar ƴan sanda a jihar Taraba, sun ceto wasu mutane uku da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su.

Jami'an ƴan sandan sun ceto mutanen ne a Dutse Mubayu, kusa da tsaunin Kona na Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

'Yan sanda sun ceto mutane a Taraba
'Yan sanda sun kubutar da mutanen da aka sace a Taraba Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Abdullahi Usman ya fitar, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga, sun kubutar da mutane kusan 20

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun ƙubutar da mutane a Taraba

Kakakin ƴan sandan ya ce an yi garkuwa da mutanen guda uku ne a ƙauyen Sibre na ƙaramar hukumar Ardo Kola a ranar 6 ga watan Disamba, 2024, rahoton The Guardian ya tabbatar.

"A ranar 6/12/24 da misalin ƙarfe 2:30 na dare. An samu kiran gaggawa kan cewa an yi garkuwa da mutane uku a ƙauyen Sibre na ƙaramar hukumar Ardo Kola."
"Tawagar jami’an rundunar ƴan sanda yankin Jalingo tare da hadin gwiwar ƴan banga sun kai ɗauki tare bin sahun masu garkuwa da mutanen"
"Ƴan bindigan sun yi artabu da tawagar jami'an tsaron a Dutse Mubayu kusa da tsaunin Kona. Saboda ƙarfin ƴan sanda, miyagun sun tsere inda suka bar mutanen da suka sace."
"An kuɓutar da wadanda lamarin ya rutsa da su ba tare da sun ji rauni ba, kuma an sake haɗa su da iyalansu."

- Abdullahi Usman

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi bajinta, sun tsallake cin hancin $17,000 daga hannun 'yan damfara

Kakakin ƴan sandan ya kuma ce an ƙwato wata jigida ta bindiga ƙirar AK-47 ɗauke da harsasai guda 35.

Ƴan sanda sun daƙile harin ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan jihar Katsina sun samu nasarori a wasu hare-haren da ƴan bindiga suka kai.

Ƴan sandan sun ɗaƙile yunƙurin sace mutanen da ƴan bindiga suka yi a wasu ƙananan hukumomi guda biyu na jihar Katsina.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng