Abba Zai Biya Kudin Makarantar Talakawan da Ganduje Ya yi Biris da Su
- Abba Kabir Yusuf ya kai ziyara birnin Lefkosia na kasar Cyprus domin tattaunawa da mahukuntan jami’ar Near East kan daliban Kano
- Dalibai da suka kammala karatu tsakanin 2015 zuwa 2019 suna fuskantar tsaiko wajen samun takardunsu saboda bashin kudin makaranta
- Rahotanni sun tabbatar da cewa an cimma matsayar magance matsalar kuma gwamnan ya yi alkawarin ci gaba da ba ilimi muhimmanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Cyprus - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyara kasar Cyprus domin tattaunawa kan matsalar rashin fitowar takardun karatu na daliban Kano.
Gwamnatin Kano ta bayyana cewa lamarin ya shafi daliban da suka kammala karatu a Jami’ar Near East tsakanin 2015 zuwa 2019.
Abba Kabir ya wallafa a Facebook cewa matsalar ta taso ne sakamakon bashin kudin makaranta da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kasa biyan jami’ar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin ziyarar, gwamnan ya bayyana damuwarsa kan yadda batun ya zama cikas ga rayuwar daliban da kuma ci gaban jihar Kano.
Daliban da aka gaza biyawa kudin makaranta
Daliban Kano da suka kammala karatun likitanci, unguzoma, da sauran fannoni a Cyprus sun gaza samun takardun shaidarsu sakamakon rashin biyan kudin makaranta.
Lamarin ya jefa daliban cikin halin rashin samun damar aikin gwamnati ko ci gaba karatu a sauran matakai.
Abba Kabir ya ce matsalar ta jawo babban koma baya ga burin daliban Kano da ke fatan samun ci gaba a rayuwarsu da kuma jihar da ke bukatar kwararru irin su.
Matakin da gwamna Abba Kabir ya dauka
A yayin taron da ya gudana da mahukuntan Jami’ar Near East, an cimma matsaya kan yadda za a biya bashin kudin makarantar da ya yi sanadiyyar tsaikon fitar da takardun daliban
Abba Kabir ya nuna farin cikinsa kan yadda tattaunawar ta kasance, yana mai jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da sanya ilimi da jin dadin al’umma a sahun gaba.
Gwamna Abba ya ziyarci daliban Kano a Indiya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamna jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yabawa ƙwazon ɗaliban da ya ta tura karatu kasar Indiya.
An ruwaito cewa a wata ziyara da ya kai musu, Abba Kabir Yusuf ya tattauna da daliban kan ƙalubale da nasarorin da suka samu yayin karatu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng