Sarkin Musulmi Ya Yi Ta'aziyyar Sheikh Muyideen Ajani, Ya Fadi Rashin da Aka Yi

Sarkin Musulmi Ya Yi Ta'aziyyar Sheikh Muyideen Ajani, Ya Fadi Rashin da Aka Yi

  • Mai alfarma Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bi sahun masu alhini kan rasuwar sanannen malamin addinin musulunci a jihar Oyo
  • Sarkin Musulmin ya yi ta'aziyyar Sheikh Muyideen Ajani Bello wanda ya koma ga mahaliccinsa a ranar Juma'a, 6 ga watan Disamban 2024
  • Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ga al'ummar musulmin jihar Oyo da ƙasa baki ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Oyo - Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi alhinin rasuwar Sheikh Muyideen Ajani Bello.

Sarkin musulmin ya yi ta’aziyyar rasuwar Sheikh Muyideen Ajani Bello wanda ya kwashe shekaru yana wa'azi.

Sarkin Musulmi ya yi ta'aziyyar rasuwar Sheikh Muyideen
Sarkin Musulmi ya yi alhinin rasuwar Sheikh Muyideen Ajani Bello Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sashen kula da ƴada labarai na Sarkin Musulmin ya fitar, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Muyideen Ajani Bello ya rasu ne a safiyar ranar Juma’a, 6 ga watan Disamba, 2024, kuma tuni aka yi jana’izarsa a mahaifarsa da ke birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Bayan Faransa, gwamnatin Tinubu ta kulla sabuwar yarjejeniya da kasar Pakistan

Sarkin Musulmi ya yi jimamin rasuwar Sheikh Muyideen

Sarkin musulmin ya bayyana marigayi malamin addinin musuluncin a matsayin mutum nagari kuma mai halin yin wa'azin.

"Ba mu da wani zaɓi face mu yarda da rasuwarsa a matsayin nufi daga Allah."
"Rasuwar Sheikh Muyideen Ajani Bello rashi ne ga al'ummar musulmin Najeriya musamman al'ummar musulmin yankin Kudu maso Yammacin Najeriya da al'ummar musulmin jihar Oyo."
"Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya karɓi ayyukansa nagari a matsayin ibada, Ya sanya shi a Al-Jannah Firdaus. Amin."

- Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III

Tinubu ya yi ta'aziyyar Sheikh Muyideen Ajani

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasan Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sheikh Muhyideen Ajani Bello, malamin da ya sadaukar da kansa wajen yi wa addinin Musulunci hidima.

Shugaban ƙasan ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai hazaka, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen bautar Allah da yada koyarwar Alkur’ani mai girma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng