Shugaban Masu Garkuwa da Mutane, Idris Alhaji Jaoji Ya Shiga Hannu

Shugaban Masu Garkuwa da Mutane, Idris Alhaji Jaoji Ya Shiga Hannu

  • Rundunar ‘yan sanda ta ceto mutanen da aka sace a Katsina, Akwa Ibom, Rivers, da Taraba, tare da kama wadanda ake zargi da laifuffuka
  • An samu nasarar kwato makamai da dama, ciki har da bindigu kirar AK-47, rigar kariya daga harsasai, da kayan sojoji a jihohi
  • Haka zalika rundunar ta yi nasarar cafke wani shugaban masu garkuwa da mutane tare da mai ba 'yan bindiga bayanai a jihar Taraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta samu gagarumar nasara wajen yaki da laifuffukan fashi da makami, garkuwa da mutane da sauransu.

Samamen da 'yan sanda suka gudanar a jihohin Katsina, Akwa Ibom, Rivers, da Taraba sun kai ga kubutar da wadanda aka sace, kama masu laifi, da kwato makamai masu yawa.

Kara karanta wannan

Sojoji, 'yan sanda da 'yan banga sun hadu sun gwabza da tulin 'yan bindiga

Yan sanda
Yan sanda sun ceto mutane a jihohi. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Rundunar 'yan sanda ta wallafa a Facebook cewa IGP Kayode Egbetoku ya tabbatar da cewa za su ci gaba da daukar matakai na musamman domin tabbatar da tsaro a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan sanda sun ceto mutane 20 a Katsina

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa ‘yan sanda sun ceto mutane 20 da aka yi yunkurin sacewa a wurare daban-daban a jihar Katsina.

A ranar 7 ga Disamba, jami’an ‘yan sanda sun fatattaki ‘yan bindiga a hanyar Katsina-Magamar Jibia, inda suka yi nasarar kubutar da mutane 10.

Haka zalika, jami’an sun dakile wani yunkurin garkuwa da mutane 10 a kan hanyar Funtua-Gusau bayan musayar wuta da 'yan bindiga.

An kama shugaban masu garkuwa

A Taraba, an fatattaki tawagar masu garkuwa a Dutsen Mubayu, inda suka ceto mutane uku tare da kama wani shugaban masu garkuwa, Idris Alhaji Jaoji, da mai bayar da bayanai.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza kazamin fada da 'yan bindiga, an kwato motar 'yan ta'adda

Haka zalika a jihar Rivers, an kubutar da wani yaro dan shekara 10, Emmanuel John bayan an sace shi.

A jihar Akwa Ibom, jami’ai sun ceto mutane biyu a wani harin da aka kai a kauyukan Amayam da Ikot Ukpong, tare da kashe wasu ‘yan ta’adda biyu.

Yan sanda sun kama 'yan fashi da makami

Rundunar ‘yan sanda ta kama wata tawagar masu fashi da makami a kan hanyar Makurdi-Lafia a jihar Benue.

An kama ‘yan tawagar guda takwas tare da kwato bindigu kirar G-3, kayan sojoji, takalmin sojoji, harsasai, da wasu kayan fada.

An fatattaki 'yan ta'adda a jihohin Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Najeriya sun kaddamar da farmaki a kan wasu 'yan ta'adda a jihohin a Taraba da Benue.

An ruwaito cewa sojojin sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindiga a wasu yankuna na jihohin tare da kwato kayan fada da dama ciki har da mota.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng