Gwamna Ya Fusata ASUU, Malaman Jami'a Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani
- Kungiyar ASUU reshen jami'ar Legas ta tsunduma yajin aiki kan gazawar gwamnatin jihar na aiwatar da karin albashin malaman
- Yajin aikin ya samu goyon bayan kwamitin hadin gwiwar kungiyoyin ma’aikatan jami’a, ciki har da NASU, SSANU da NAAT
- Malaman jami'ar sun koka kan bambancin albashi da ake samu tsakanin jami’o’in jihar Legas, tana bukatar daidaito cikin adalci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) reshen jami’ar jihar Legas (LASU), Ojo, ta ce ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.
Kungiyar ASUU reshen jami’ar LASU ta shiga yajin aikin ne saboda rashin biyan karin albashi da aka amince da shi tun a Janairun 2023.
ASUU ta shiga yajin aiki a jami'ar LASU
Premium Times ta rahoto cewa malaman jami'ar LASU sun fara yajin aikin daga ranar 6 ga watan Disamba kamar yadda shugaban kungiyar, Farfesa Ibrahim Bakare ya sanar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 8 ga watan Disamba, Farfesa Bakare ya ce abin takaici ne yadda gwamnatin jihar ta gaza aiwatar da karin albashin ga 'yan ASUU.
Farfesa Bakare ya yi nuni da cewa tuni an riga an fara aiwatar da wannan karin albashi a duk jami’o’in tarayya da wasu jami’o’i 18 na jihohi.
ASUU-LASU ta bayyana cewa yajin aikin ya samu hadin kan kungiyoyin ma’aikatan jami’ar (JAC) da suka hada da NASU, SSANU, da NAAT
Ƴan ASUU sun gabatar da bukata ga gwamnati
Akwai bukatar gwamnati ta daidaita albashin malamai da na jami’o’in fasaha da ilimi na jihar Legas, kamar yadda kungiyar ta nemi a yi a cewar rahoton The Nation.
Kungiyar ta koka kan gazawar gwamnati wajen aiwatar da shawarwarin wani kwamiti da aka kafa kan batun daidaita albashin malaman jami'ar jihar.
ASUU-LASU ta yi kira ga dalibanta da su kasance masu hakuri da fahimta yayin da suke jiran matakin da gwamnatin jihar za ta dauka nan gaba.
Kungiyar ta kuma bukaci gwamnati ta dauki mataki cikin gaggawa don magance wannan matsala da kuma dawo da walwala a jami'ar LASU.
Gwamna ya ba dalibi kyautar N10m
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya gwangwaje wani dalibin jami'ar jihar Legas (LASU) da kyautar Naira miliyan 10.
Dalibin mai suna Olaniyi Olawale ya samu kyautar N10m saboda ya kammala karatunsa na ilimin akanta da makin CGPA 4.98, wanda ya zamo mafi hazaƙa a jami'ar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng