An Gano Dalilin Wasu Ƴan Najeriya na Baƙin Ciki da Farfaɗowar Naira
- Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya soki ƴan kasar nan ba su fata mai kyau ga ci gaban darajar Naira a kasuwar canji
- Ya bayyana haka ne a lokacin da darajar Naira ta jera kwanaki biyu ta na samun kanta a kasuwar musayar kuɗaɗe
- Fasto Omokri, ya yi fatan darajar kuɗin ƙasar nan za ta ci gaba da ɗaukaka duk da dalilan wasu na ƙin ci gaban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Reno Omokri, tsohon hadimin shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana rashin jin daɗinsa a kan yadda wasu ba sa murna da farfaɗowar darajar Naira.
A ƴan kwanakin nan ne darajar Naira ta fara dawowa hayyacinta a kasuwar musayar kuɗaɗen ƙasashen ƙetare, inda aka canjar da Dala daya a kan N1,555.
A saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Reno Omokri ya bayyana abin da ya sa wasu ke baƙin ciki da da Naira ta fara samun kanta a kasuwar canji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Ana bakin cikin darajar Naira," Omokri
Lauya kuma marubuci, Reno Omokri ya shaida cewa wasu daga cikin ƴan Najeriya sun sayi Dala da 'Pounds' da zummar Naira za ta ci gaba da faduwa.
Ya bayyana cewa wannan na daga cikin dalilan da ya sa ba sa murna da samuwar darajar kuɗin ƙasarsu a shafukan sada zumunta.
'Naira za ta haɓaka," Omokri
Tsohon hadimin shugaban ƙasa Jonathan, Reno Omokri ya bayyana fatan da wasu ƴan Najeriya ke yi da cewa ba zai yi tasiri ba.
Ya bayyana fatansa na cewa darajar Naira za ta ci gaba da dawowa hayyacinta a lokacin da wasu ke fatan kuɗin zai ci gaba da faɗuwa warwas.
Darajar Naira na farfaɗowa
A wani labarin, kun ji cewa darajar Naira na ci gaba da bayar da mamaki a kasuwar canjin kuɗaɗe, inda ta jera kwanaki biyu ta na farfaɗowa ba kamar da ba.
Rahotanni sun bayyana cewa a cikin watanni shida da su ka gabata, ba a taɓa sayar da Dala a kan N1600, amma a baya bayan nan har an sayar da Dala a kan N1500.
Asali: Legit.ng