Gwamnati: "Malamai da Dattawan Arewa na Goyon Bayan Kudirin Harajin Tinubu"
- Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, ya ce babu gaskiya a zargin cewa 'yan Arewa na adawa da kudirin gyaran haraji
- Sanata Akume ya ce ya tuntubi manyan dattawa, shugabanni da malamai daga Arewacin Najeriya, kuma sun nuna goyon bayansu ga shirin
- Akume ya kara da cewa gwamnati ta yi garambawul kan tsarin raba kudin VAT a kudirin, wanda zai amfanar da jihohin Arewa sosai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, ya wanke kudirin gyaran haraji daga zargin cewa an yi niyya ne domin durkusa yankin Arewa.
Sanata Akume ya bayyana cewa ya tattauna da wasu shugabanni da dattawan Arewa, kuma babu wani da ya nuna adawa da kudirin, sai ma goyon baya da suka yi.
Da yake magana a wani shirin talabijin na TVC News ranar Lahadi, Akume ya bayyana cewa batun adawa da kudirorin haraji daga yankin Arewa ba gaskiya ba ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akume: Ba za a cuci Arewa ba kan haraji
Sanata Akume ya karyata zargin cewa kudirin gyaran haraji na neman cutar da yankin Arewa, inda ya ce:
“Mutane suna cewa wai kudirin zai cuci wani yanki (Arewa). To, ni ma daga wannan yankin nake, kuma ina goyon bayan kudirin dari bisa dari.
Na tattauna da shugabanni da dattawan Arewa, babu wanda ya nuna adawa da kudirin."
- Sanata George Akume
Punch ta wallafa cewa Akume ya yi zargin cewa wasu suna amfani da batun kudirin haraji domin manufofin siyasa, musamman domin samun goyon baya a zaben 2027.
Arewa za ta fi amfana inji Akume
Sanata Akume ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta rage kashi 5% daga rabon da take samu daga kudaden VAT, ta kara shi ga jihohi da kananan hukumomi.
“Idan aka duba tsarin VAT a kudirin, jihohi za su samu kashi 55%, yayin da kananan hukumomi za su rika karbar kashi 35%.
Wannan shi ne tsarin da zai kawo karin kudade ga jihohi da kananan hukumomi, musamman a Arewa da ke da jihohi da kananan hukumomi masu yawa.”
- Sanata George Akume
A karshe, Akume ya yi kira ga jama’a da su guji zanga-zanga marasa tushe, maimakon haka su bi hanyoyin da doka ta tanada domin bayyana ra’ayoyinsu a kan kudirin.
An kafa sharadin yarda da kudirin haraji
A wani rahoton, kun ji cewa manyan kungiyoyin dattawa da matasan Arewa sun magantu kan sharudan janye adawarsu da kudirin haraji.
Legit Hausa ta ruwaito cewa kungiyoyin sun kafa sharuda ga gwamnatin Tinubu domin duba yiwuwar amincewa da kudirin harajin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng