"A Fara daga sama," Obasanjo Ya Fadi Yadda Za a Yi Nasarar Maganin Rashawa
- Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya ce sai an fara maganin cin hanci da rashawa daga kan shugabanni
- Tsohon shugaban na Najeriya ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi a kan ayyukansa ga ƙasar nan
- Ya shawarci masu ruwa da tsaki a kan hanyar da za su bi wajen tabbatar da kawo ƙarshen matsalar rashawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Osun - Tsohon shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana takaicin yadda cin hanci da rashawa ta ratsa dukkanin sassan ƙasar nan.
Ya bayyana mummunan lamarin da maciji mai kawuna da dama, ana ƙoƙarin magance shi ta wannan hanya, ya na ƙara girma ta wani sashen.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Cif Olusegun Obasanjo ya ce akwai babbar hanya daya da kasar nan za ta iya kawo ƙarshen cin hanci da rashawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Olusegun Obasanjo: "Yadda za a magance rashawa"
Jaridar Punch ta ruwaito tsohon shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo ya ce sai a yaƙi cin hanci da rashawa daga shugabanni kafin a yi nasarar kawar da ita.
Ya fadi haka ne ta taron 'zoom' da aka gudanar a daren Lahadi mai taken 'Boiling Point Arena' , inda aka tattauna ci gaban da Obasanjo ya kawo ƙasar nan.
"Za a iya magance rashawa," Obasanjo
Cif Olusegun Obasanjo, wanda ya yi shugabancin ƙasar nan a mulkin soja da farar hula ya ce dole a dage da yaƙar cin hanci da rashawa a kullum a tsakanin jama'a.
Cif Obasanjo ya kuma caccaki shugabannin da ke gwamnati bisa zarginsu da ƙirƙiro wa jama'a talauci a Najeriya.
Cif Obasanjo ya fadi dalilin rashin ci gaba
A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya yi zargi cin hanci da rashawa ne babban abin da ya hana ƙasa ci gaban da ake buƙata.
Cif Obasanjo ya ce duk da ya yi kokari a gwamnatinsa don ganin an kawo kan matsalar cin hanci da rashawa, amma ta zama gagarumar matsala ce da sai an kawar da ita.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng