Najeriya da Kasashen Waje Sun Fara Luguden Wuta domin Murkushe Lakurawa
- Rundunar Sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar wasu ƙasashe makwabta sun fara sintirin bai-ɗaya domin murkushe Lakurawa
- Mazauna jihar Sokoto sun bayyana damuwa kan yadda iyakokin Najeriya suke ba da damar karuwar rashin tsaro
- An kafa sansanonin wucin gadi a wasu wuraren da Lakurawa suka yi wa barazana domin tabbatar da tsaron yankunan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Rundunar Sojojin Najeriya da takwarorinsu daga ƙasashen Chadi, Nijar, da wasu makwabta sun ƙaddamar da hare-haren bai-ɗaya domin murkushe Lakurawa.
Hakan na zuwa ne yayin da ake zargin cewa ƙungiyar Lakurawa ta kafa sansanoni a kan iyakokin Najeriya da Nijar, inda take gudanar da ayyukanta.
Punch ta wallafa cewa rundunar sojojin Najeriya, tare da haɗin guiwar makwabta, sun fara sintirin bai-ɗaya don dakile motsin ƙungiyar a iyakokin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daraktan yada labaran rundunar tsaro, Manjo-Janar Edward Buba ya ce suna aiki tare da ƙasashen maƙwabta domin rufe ɓangarorin iyakoki da suke bai wa masu aikata laifi damar shiga Najeriya cikin sauki.
An kwato wurere daga hannun Lakurawa
Rundunar Sojojin Najeriya ta tabbatar da kafa sansanoni na wucin gadi a yankunan da ƙungiyar Lakurawa ta yi wa illa.
Wani jami’in soja ya bayyana cewa a halin yanzu, akwai zaman lafiya a yankunan da Lakurawa suka riga suka kwace a baya.
Manjo-Janar Edward Buba ya ce sintirin bai-ɗaya tsakanin Najeriya da ƙasashen maƙwabta zai taimaka wajen toshe manyan ɓangarorin da suke ba wa ‘yan ƙungiyar damar kai hare-hare.
Barazanar tsaro a iyakokin Najeriya
Wasu ƙwararru a fannin tsaro sun bayyana cewa yawancin ƙauyukan da ke fama da rashin tsaro a jihar suna da iyaka da ƙasashen waje ko kuma wasu jihohin ƙasar.
Saboda haka aka bukaci hukumomi su tabbatar da cewa an tsaurara tsaro a waɗannan yankunan da ke kan iyaka.
'Yan ta'adda sun sace amarya a Sokoto
A wani rahoton, kun ji cewa yaran dan bindiga Bello Turji sun sace amarya tare da wasu kawayenta hudu a jihar Sokoto.
An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a Kwaren Gamba kusa da Kuka Teke, wani kauye da ya dade yana fama da hare haren 'yan bindiga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng