Tirkashi: Alkalan Kotu Sun Tsunduma Yajin Aiki, Sun Zayyanawa Gwamnati Bukatu 8

Tirkashi: Alkalan Kotu Sun Tsunduma Yajin Aiki, Sun Zayyanawa Gwamnati Bukatu 8

  • Alakalai a Cross River sun tsunduma yajin aiki bayan gwamnatin jihar ta gaza aiwatar da wasu bukatu takwas da suka gabatar
  • Kungiyar alakalan majistire ta ce gwamnatin jihar ta ki biyan bukatunsu duk da cewa sun tura wasiku da zama kan yajin aikin
  • An bukaci alkalan majistire a jihar da su tsaya daram wajen bin dokar yajin aikin, domin tilasta gwamnati biyan bukatunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Cross River - Alkalan kotun majistire a jihar Cross River sun shiga yajin aiki na sai baba-ta-gani saboda gazawar gwamnati na biyan bukatu takwas da suka gabatar.

Kungiyar alkalan majistire ta Najeriya reshen jihar ta bayyana hakan a sanarwa da shugabansu Godwin Onah da sakatarenta Solomon Abuo suka sa wa hannu.

Alkalai sun yi magana yayin da suka tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a Cross Rivers
Alkalan kotunan majistire a jihar Cross Rivers sun shiga yajin aikin sai baba ta gani. Hoto: High Court of Justice, Lagos
Asali: UGC

Alkalan majistire sun tsunduma yajin aiki

Alkalan sun tsunduma yajin aikin ne saboda rashin biyan bukatunsu da suka shafi walwala, karin girma da haɓaka yanayin aikin su, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Ana cikin halin wahala, Gwamna zai cika kasuwanni da shinkafa mai rahusa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar alkalan ta sanar da cewa yajin aikin zai cigaba har sai gwamnatin jihar ta cika dukkanin alkawuran da ta daukar masu a kan bukatunsu.

Yajin aikin ya biyo bayan watannin da aka shafe ana tattaunawa tsakanin alkalan da gwamnatin jihar wadanda ba su haifar da da mai ido ba.

Abin da ya faru kafin shiga yajin aikin

the Nation ta rahoto cewa kungiyar alkalan ta fara gabatar da bukatunsu ga gwamnati a taron da suka yi a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2024.

Sun kuma aika da wata wasika ga gwamna a ranar 11 ga watan Nuwamba, tare da tsawaita wa'adin sanarwar yajin aikin har zuwa 22 ga watan Nuwamba.

Duk da wannan, gwamnati ta kasa daukar matakin tattaunawa, don haka kungiyar ta umurci alkalan da su dakatar da aiki har sai an biya bukatun su.

NLC ta hana alkalai zaman kotu

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta hana alkalai gudanar da zaman kotu a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ji kukan ƴar NYSC da malama ta lakadawa duka a Ilorin, ya dauki mataki

An ce ma'aikatan da ke aiki a cikin kotun da ke karkashin kungiyar kwadagon ne suka hana alkalai zaman kotu saboda yajin aikin da NLC ta shiga na gama gari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.