Yadda Sabuwar Dokar Fintiri na Kirkirar Masarautu Ta Kassara Ikon Atiku da Lamido
- Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya rattaba hannu kan sabuwar dokar da ta samar da sababbin masarautu
- Gwamnan tun farko ya tura kudirin ne gaban Majalisar dokokin jihar wacce ta tattauna tare da sahale masa
- Sai dai wasu na ganin samar da sababbin masarautun guda 83 za su dakile karfin ikon Atiku Abubakar da Lamidon Adamawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya rattaba hannu kan dokar kirkirar sababbin masarautu.
Hakan ya biyo bayan tura kudirin Makalisar jihar wanda ta samar da sababbin masarautu har giuda 83.
Gwamna Fintiri ya samar da sababbin masarautu
Premium Times ya ce hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da aka tura majalisar dokokin jihar a ranar 2 ga Disambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya nemi soke tsohuwar dokar tare da sake fasalin dokar kirkirar masarautu ta jihar Adamawa ta 2024 domin samar da cikakken tsari.
Majalisar dokokin jihar ta tattauna kan kudirin dokar na tsawon rana guda kuma ta amince da shi, daga bisani Gwamna Fintiri ya rattaba hannu kan dokar da zimmar inganta mulki da magance matsalolin tsaro.
Sai dai masu lura da al’amura sun ce sabuwar dokar na da nufin samar da karin masarautu tare da nada sabbin sarakuna ajin farko a jihar.
Yadda dokar masarautu za ta dakile Atiku, Lamido
Dokar ta rage tasirin Lamidon Adamawa, Mustapha Barkindo ta hanyar rage yawan kananan hukumomin da ke karkashinsa daga takwas zuwa uku.
Masarautar Adamawa a baya ta kunshi kananan hukumomin Hong da Song da Gombi da Fufore da Girei da Yola ta Arewa da Yola ta Kudu da Mayo-Belwa.
Amma karkashin sabuwar dokar, masarautar yanzu za ta kula da Girei da Jimeta da Yola kawai, cewar Daily Post.
Haka, Atiku Abubakar wanda ke rike da sarautar Waziri kuma babban mai nadin sarakuna, zai yi iko ne kawai a kananan hukumomi uku.
Har ila yau, dokar za ta taɓa Sarkin Mubi, Abubakar Isa-Ahmadu da masarautar Bachama karkashin ikon Homun Daniel-Shaga.
Gwamna Okpebholo ya rushe sababbin masarautu
Kun ji cewa Gwamnatin jihar Edo ta dauki wasu muhimman matakai kan sababbin masarautu da wata cibiyar al'adu.
Gwamna Monday Okpebholo shi ya dauki matakin inda ya dawowa Oba na Benin, Oba Ewuare II martabarsa yadda take a baya.
Asali: Legit.ng