An Shiga Tashin Hankali da Malamin Addini Ya Bata, An Bukaci Addu'o'i

An Shiga Tashin Hankali da Malamin Addini Ya Bata, An Bukaci Addu'o'i

  • Al'ummar jihar Anambra sun shiga jimami bayan bacewar wani babban malamin addinin Kirista a ranar Juma'a
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa Rabaran Godwin Okpala ya bace yayin da yake kan hanyar zuwa garin Umuchu
  • Sai dai da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda, SP Tochukwu Ikenga ya ce bai samu labarin faruwar lamarin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra - An shiga tashin hankali a jihar Anambra bayan bacewar wani malamin addinin Kirista.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Rabaran kuma Farfesa Godwin Okpala ya bace ba a san inda yake ba.

An nemi malamin addini an rasa a Anambra
Fitaccen Fasto, Godwin Okpala ya bata bat a jihar Anambra. Hoto: Legit.
Asali: Original

Fitaccen Fasto a Anambra ya bace

Tribune ta ce an ga Rabaran Okpala a karon karshe a ranar Juma’a 6 ga watan Disambar 2024 lokacin da ya tashi tafiya zuwa Umuchu a jihar.

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito kan 'dalilin' mamaye fadar Sanusi II, an ce hakan ka iya zama alheri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai bai isa inda ya nufa ba kuma duk kokarin da aka yi na samun labarinsa ya ci tura.

Babban Faston a garin Nnewi, Ndubuisi Obi ya fitar da sanarwa a ranar Asabar 7 ga watan Disambar 2024.

Ana bukatar addu'o'i kan bacewar Fasto

Faston ya bukaci mutane su taya su addu’a domin samun nasarar dawo da Faston lafiya.

Sanarwar ta bayyana cewa Rabaran Okpala yana tare da direbansa lokacin kafin faruwar lamarin inda shi ma direban bai dawo ba.

“Muna rokonku sosai da ku taya mu addu’o’in neman kariya da dawowarsu lafiya."
"Mun tuntubi hukumomin da suka dace, kuma muna da fata tare da dogara ga ikon Allah domin samun mafita mai kyau.”

- Fasto Ndubuisi Obi

Sai dai rundunar yan sanda ta bakin kakakinta, SP Tochukwu Ikenga ya ce bai samu labarin faruwar lamarin ba.

Yan bindiga sun hallaka yan banga a Anambra

Kun ji cewa jami'an tsaro na ƴan banga sun fuskanci wani hari daga wajen ƴan bindiga a jihar Anambra a 'yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Ana jimamin rasa rayuka a Zamfara, ana zargin 'bam' ya tarwatse da wani a Niger

Yan bindigan sun kai wa ƴan bangan hari a ranar Lahadi, 24 ga watan Nuwamban 2024 inda suka raunata mutum ɗaya.

Rundunar ƴan sandan jihar Anambra ta hannun kakakinta, SP Tochukwu Ikenga ya tabbatar da kai harin da ƴan bindigan suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.