Gwamnan Neja Ya Shirya Runtuma Kora, An Bayyana Ma'aikatan da Abin Zai Shafa
- Gwamnatin Neja za ta kori malaman da ba su cancanta ba daga aiki yayin da za ta tantance malaman domin inganta ilimin jihar
- Kwamishiniyar ilimin firamare, Dakta Hadiza Mohammed ta ce daga yanzu ba kowa ne gwamnati za ta yarda ya zama malami ba
- A yayin taron tsofaffin daliban GSS Bida da ya gudana a Minna, an karrama manyan tsoffin dalibai ciki har da Abdulsalami Abubakar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - Gwamnatin Neja ta ce tana shirin korar malaman da ba su cancanta ba daga makarantu domin inganta koyarwa da karatu a jihar.
An kuma umarci tsofaffin malamai da ke zaune a gidajen ma’aikata na makarantu da su bar gidajen ga sabbin malamai da za su kama aiki.
Kwamishiniyar ilimin firamare, Dakta Hadiza Asabe Mohammed, ta bayyana hakan a taron shekara-shekara na tsofaffin daliban GSS Bida da aka yi a Minna, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Neja za ta kori malamai
Ta sanar da cewa gwamnatin jihar ba za ta lamunci daukar malaman da basu cancanta aiki ba, kuma duk malamin da bai tsallake tantancewar ba za a sallame shi.
"Jihar ba za ta kara yarda kowa ya fada harkar koyarwa ba. Za a yiwa malamai tantancewa mai tsanani. Wadanda suka gaza tsallakewa za a sallame su."
- A cewar kwamishiniyar.
Sai dai Dakta Hadiza ta ce malaman da kungiyar PTA ta dauka aiki za su ci gaba da aikinsu idan sun wuce tantancewa. Ta ce za a dawo da tsarin National Career Path.
An karrama Janar Abdulsalmi Abubakar
Shugaban tsofaffin daliban GSS Bida, Janar Abdulmalik Halidu Giwa, ya ce tsofaffin dalibai sun yi gyare-gyare a makarantar amma makarantar na bukatar karin tallafi.
Shugaban kwamitin shirye-shirye, Alhaji Muhammadu Agwai, ya bayyana damuwa kan lalacewar makarantar tare da neman goyon bayan 'yan kungiyar don kare ta daga rugujewa.
A taron, an karrama tsoffin dalibai na musamman, ciki har da Janar Abdulsalami Abubakar da Kanal Sani Bello da wasu mutane 15.
Asali: Legit.ng