'Yan Sanda Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane Kusan 20
- Jami'an rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar Katsina sun samu nasarar daƙile yunƙurin ƴan bindiga na yin garkuwa da mutane
- Ƴan sandan sun hana ƴan bindigan yin garkuwa da mutane a ƙananan hukumomin Faskari da Jibia
- Kusan mutane 20 aka ceto waɗanda ƴan bindigan suka yi yunƙurin yin garkuwa da su zuwa cikin daji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Katsina sun yi nasarar daƙile yunƙurin ƴan bindiga na yin garkuwa da mutane.
Ƴan sandan sun daƙile yunƙurin na ƴan bindigan ne a ƙananan hukumomin Faskari da Jibia na jihar.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda sun ceto mutanen da aka sace
Kimanin mutane 20 da aka yi garkuwa da su ne aka kuɓutar, bayan da ƴan sanda suka daƙile yunƙurin sace su da ƴan bindigan suka yi.
Kakakin ƴan sandan ya ce harin farko ya faru ne a ranar 7 ga watan Disamba, 2024, a Kwanar Makera da ke kan hanyar Katsina zuwa Magamar Jibia, a ƙaramar hukumar Jibia.
Ya ce ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai irin su AK-47, sun buɗe wuta kan wata mota, inda suka yi yunƙurin sace mutanen da ke cikinta.
Yadda ƴan sanda suka daƙile harin ƴan bindiga
Ya bayyana cewa jami’an ƴan sanda na Jibia, da suka samu labarin, sun kai ɗauki tare da yin artabu da ƴan bindigan, inda suka tilasta musu fasa sace mutanen yayin da suka gudu ɗauke da harbin bindiga.
"An yi nasarar ceto dukkanin mutane 10 da ke cikin motar ba tare da sun ji rauni ba."
"A wani lamari makamancin haka a wannan ranar, a Marabar Bangori dake kan titin Funtua- Gusau a ƙaramar hukumar Faskari, wasu ƴan bindiga sun kai farmaki kan wata mota da ke ɗauke da fasinjoji."
"Jami’an rundunar ƴan sandan da aka sanar da lamarin, sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka yi artabu da ƴan bindigan."
"Saboda ƙarfin ƴan sandan, ƴan bindigan sun tsere inda aka samu nasarar ceto dukkanin fasinjojin."
- ASP Abubakar Sadiq Aliyu
Ƴan sanda sun samu yabo
Muhammad Kabir wani mazaunin jihar Katsina ya bayyyana Legit Hausa cewa abin da ƴan sandan suka yi abin a yaba ne.
"Eh gaskiya sun yi ƙoƙari sosai wajen kuɓutar da mutanen. Abin da suka yi abin a yaba ne, muna yi musu addu'ar Allah ya ci gaba da ba su nasara kan miyagu."
- Muhammad Kabir
Ƴan bindiga sun farmaki ƙauyuka
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Kankara da ke jihar Katsina.
Ƴan bindigan a yayin harin sun hallaka mutane takwas tare da raunata wasu da dama, sannan suka yi garkuwa da wasu mutane masu yawa.
Asali: Legit.ng