An Samu Asarar Rai bayan Barkewar Rikici tsakanin Matasa da Makiyaya a Arewa
- An samu ɓarkewar rikici tsakanin matasa da wasu makiyaya a ƙaramar hukumar Yamaltu-Deba ta jihar Gombe
- Rikicin wanda ya fara sakamakon tare hanyar da wasu matasa suka yi ya jawo mutum ɗaya ya rasa ransa
- Rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta bayyana ƙoƙarin da ta yi wajen shawo kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Gombe - Rikici ya ɓarke tsakanin makiyaya da matasa a ƙauyen Lano da ke ƙaramar hukumar Yamaltu Deba a jihar Gombe.
Ɓarkewar rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya tare da kwantar da wasu mutum biyu a asibiti.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Gombe, ASP Buhari Abdullahi, a cikin wata sanarwa ya tabbatar da aukuwar rikicin na ranar Asabar, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda rikicin matasa da makiyaya ya auku
A cewar sanarwar, rikicin ya fara ne a lokacin da wasu matasa daga ƙauyen Lano suka tare hanyar Lano-Deba, inda suka kai hari kan makiyayan da ke wuce zuwa ƙauyen Kuri, sannan suka kashe musu shanu biyar.
Matasan sun zargi makiyayan da ƙwace wayoyin manoman yankin tare da hana safarar kayan amfanin gona, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
"Mun samu labarin cewa wasu matasa daga ƙauyen Lano sun tare hanyar Lano zuwa Deba inda suka far wa Fulani makiyaya sannan suka kashe shanunsu biyar."
"Da samun rahoton, DPO na yankin ya jagoranci wata tawaga zuwa wurin domin shawo kan lamarin."
"Sai dai duk da ƙoƙarin dawo da kwanciyar hankali, wasu daga cikin matasan sun bi makiyayan zuwa cikin daji, lamarin da ya haifar da tashin hankali.
"An harbi mutane uku da kwari da baka yayin arangamar. An garzaya da su babban asibitin Deba domin yi musu magani amma daga baya aka kai su asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke Gombe.”
"Ɗaya daga cikinsu ya rasu sakamakon raunin da ya yi a cikinsa, yayin da sauran mutum biyun ke kwance a asibiti."
- ASP Buhari Abdullahi
Rikici ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya
A wani labarin kuma, kun ji cewa mutane uku sun rasu sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a yankin Dogon Duste da ke jihar Nasarawa.
Rahotanni sun bayyana cewa garin da aka yi arangamar tsakanin manoman da makiyaya ya na a tsakanin ƙananan hukumomin Nasarawa da Toto na jihar.
Asali: Legit.ng