Majalisar Wakilai Na So a Rage Yawan Ministoci, Ta Aika Sabuwar Bukata ga Tinubu

Majalisar Wakilai Na So a Rage Yawan Ministoci, Ta Aika Sabuwar Bukata ga Tinubu

  • Majalisar wakilai karkashin kwamitinta na gyaran kundin tsarin mulki ta gabatar da bukatar rage ministoci zuwa 37
  • Idan aka amince da kudirin rage yawan ministocin zuwa 37, hakan zai rage kashe kuɗi da maimaita ayyuka a majalisar zartarwa
  • Dan majalisa daga Bauchi, Hon. Mansur Soro ya ce shugaban ƙasa zai iya amfani da sauran hukumomi don cike gibin ministocin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kwamitin majalisar wakilai kan gyaran kundin tsarin mulki na 1999 yana duba kudirin da zai iyakance ministocin shugaban ƙasa zuwa 37.

Kudirin mai suna "Gyaran tsarin mulkin 1999 domin tsayar da iyakance ministoci," yana gaban kwamitin ƙarƙashin jagorancin Benjamin Kalu.

Majalisar wakilai ta yi magana yayin da aka gabatar da bukatar rage yawan ministoci
Majalisar wakilai ta gabatar da bukatar rage yawan ministocin Najeriya zuwa 37. Hoto: @HouseNGR, @officialABAT
Asali: Twitter

Majalisa na so Tinubu ya rage yawan ministoci

'Yan majalisar Bauchi da Borno, Hon. Mansur Soro da Hon. Usman Zanna, ne suka gabatar da kudirin gyaran sashe na 147 (1) na kundin mulki a cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

"Ka da ku zauna a duhu," Gwamna ya buƙaci yan Najeriya su karanta kudirin haraji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kudirin ya nemi a rage yawan ministocin Najeriya zuwa 37 domin rage yawan ma’aikata, kashe kudi da kuma inganta ayyukan gwamnati.

A yanzu, majalisar zartarwa ta tarayya ƙarƙashin Shugaba Tinubu tana da ministoci 47, da suka kunshi manyan ministoci da kuma kanana.

Amfanin rage yawan ministoci zuwa 37

Tun da jimawa, shugaban ƙasa yana da damar nada minista daga kowace jihar Najeriya, sannan yana da damar ƙarin nadin wasu.

Hon. Mansur Soro ya ce kudirin iyakance ministocin zuwa 37 zai rage kashe kuɗi, daidaita tsarin ministoci, da rage maimaita ayyuka.

Ya yi nuni da cewa akwai jiha ɗaya da ke da ministoci hudu, yayin da wasu jihohin suke da ɗaya kawai, wanda ya ce ba adalci bane hakan.

Dan majalisa ya ba Tinubu shawara

Hon. Mansur Soro ya jaddada cewa shugaban ƙasa zai iya amfani da hukumomi da sauran ma’aikatu don nadin ƙwararru ba sai ya ƙara ministoci ba.

Kara karanta wannan

Sanatoci 16 daga shiyya 1 sun hada kai, sun goyi bayan Tinubu kan gyaran haraji

Dan majalisar na PDP ya yi adawa da batun cewa shugaban kasa na iya yanke shawarar nada ministoci fiye da biyu daga jaha daya domin amfani da kwararru.

Kwamitin majalisar karkashin Hon. Kalu yana kuma duba gyaran da zai tabbatar da kwarewar adalci a tsarin manyan jami’an majalisar tarayya.

Dalilin Tinubu na kin rage yawan ministoci

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi martani ga masu kiraye kiraye da ya rage yawan ministocinsa daga 47.

Shugaba Tinubu ya sanar da cewa ba zai iya rage yawan ministocinsa ba saboda hakan zai kawo koma baya ga ayyukan ci gaba a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.