Matasan APC Sun Taso Tinubu a Gaba, Suna So a Dawo da Shugaban SMDF da Aka Sauke

Matasan APC Sun Taso Tinubu a Gaba, Suna So a Dawo da Shugaban SMDF da Aka Sauke

  • Ƙungiyar matasan APC ta Zamfara ta fadawa Shugaba Bola Tinubu cewa Yazid Danfulani zai kawo ci gaba a hukumar SMDF da PAGMI
  • Matasan sun nemi Tinubu da ya dawo da nadin Danfulani tare da hakura da Hajiya Fatima Umaru-Shinkafi a shugabancin SMDF
  • Ƙungiyar ta jaddada mahimmancin sababbin dabaru a fannin ma’adanan ƙasar nan inda suka ce Danfulani na da kwarewar da ake so

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Ƙungiyar matasan APC ta Zamfara ta nemi Shugaba Bola Tinubu ya sake duba batun naɗin Yazid Umar Danfulani a matsayin shugaban SMDF da PAGMI.

Shugaban ƙungiyar, Hon. Muhammad Usman Gusau, ya ce Yazid Danfulani zai kawo ci gaba a fannin ma’adanan ƙasar nan.

Matasan APC a Zamfara sun yi magana yayin da Tinubu ya janye nadin Yazid Danfulani
Matasan APC a Zamfara sun bukaci Tinubu ya dawo da Danfulani a matsayin shugaban SMF/PAGMI. Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

Kungiya ta fadawa Tinubu amfanin Danfulani

A wani rahoto na Vanguard, kungiyar ta ce Danfulani ya yi fice a fannonin banki, kasuwanci, da gudanarwa kuma ya rike kwamishinan kasuwanci da masana’antu a Zamfara.

Kara karanta wannan

Bayan Faransa, gwamnatin Tinubu ta kulla sabuwar yarjejeniya da kasar Pakistan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta kuma yi nuni da cewa Danfulani ya yi karatu a Jami’ar Hertfordshire, inda ya kammala digirin BA da MA, wanda ya ƙara masa ƙwarewa.

Ta ce fannin ma’adanan Najeriya na buƙatar sabbin dabaru domin cimma burin gwamnatin Tinubu na Renewed Hope Agenda wanda Danfulani zai iya kawo wa.

Kungiyar matasa ta taso Tinubu a gaba

An ce Shugaba Tinubu ya naɗa Danfulani a ranar 6 ga Disamba, amma daga baya aka sake dawo da tsohuwar shugabar, Hajiya Fatima Umaru-Shinkafi.

Sun ce Danfulani ya cancanci jagorantar SMDF/PAGMI, domin ƙwarewarsa na da tasiri a bunkasar fannin hakar ma’adanan ƙasa.

Ƙungiyar ta ce tana fatan Shugaba Tinubu zai sake duba batun don tabbatar da cigaban fannin ma’adanan Najeriya.

Tinubu ya sabunta nadin Fatima Umaru-Shinkafi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya soke nadin Yazid Shehu Danfulani a matsayin shugaban asusun kula da harkokin haƙar ma'adanai (SMDF/PAGMI).

Bayan soke nadin da aka yiwa Danfulani, Tinubu ya kuma amince da sabunta nadin Fatima Umaru Shinkafi a matsayin shugabar SMDF/PAGMI.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.