Lauya Ya Jefawa Masu Goyon Bayan Kudirin Haraji Tambayoyi 5 da Ya Kamata Su Amsa”
- Audu Bulama Bukarti bai gamsu da kudirin da aka fito da shi da sunan gyaran tsarin haraji a Najeriya ba
- Masanin shari’ar ya ce akwai wasu tambayoyin da ya kamata masu goyon bayan kudirin su amsa tukuna
- Dr. Bulama Bukarti yana ganin saboda a kara azurta jihohin Legas da Ribas aka bijiro da sabon kudirin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Audu Bulama Bukarti kwararren masanin shari’a ne kuma wanda ya yi fice wajen kare hakkin al’umma a Najeriya.
Lauyan ya dauki lokaci ya na fadakar da al’umma musamman a game da kudirin haraji da ya jawo surutu a Arewacin kasar.
A shirin fashin baki da aka shirya a karshen makon jiya, Dr. Audu Bulama Bukarti ya jefa wasu tambayoyi game da wannan kudirin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Audu Bulama Bukarti ya ce akwai bukatar duk wanda yake goyon bayan kudirin gyaran harajin ya amsa tambayoyin nasa.
Menene ya jawo aka kawo kudirin harajin?
Masanin shari’ar yake cewa ya kamata a fara tambayar ko menene ya jawo za a yi dokar, wanene yake kukan rashin adalci.
Lauyan ya yi ikirarin jihohin Ribas da Legas ne suke kukan ba a yi masu adalci wajen rabon harajin VAT da suke tarawa.
Idan har ikirarin ya zama gaskiya, Bulama Bukarti ya ce an kawo dokar ne saboda cin moriyar wadannan jihohin ba kowa ba.
A tunaninsa babu abin da sa Legas za ta yi korafi saboda a taimakawa jihohin Kebbi ko Kano, sai dai domin lalitarta ta karu kurum.
A bidiyon da Kabiru Garba ya wallafa a Facebook, Bukarti ya nuna bai yarda za a canza salon rabon VAT da ke fifita Legas ba.
Wasu sun ce idan an yi na’am da dokar, VAT zai fi amafanar jihar da aka batar da kaya ba inda hedikwatar kamfani ta ke ba.
Ya jefa kalubale a nuna masa inda kudirin ya ce kason harajin zai fi tasiri a inda aka amfana da kaya ba wurin da kamfani yake ba.
Ya za a canza lissafin harajin VAT?
Ko da hakan kudirin ya nufa, ya kalubalanci a fada masa ma’aunin da za a yi amfani da shi wajen gane inda aka batar da kayayyaki.
Masanin dokar bai ganin akwai tsarin da za a iya bi har gwamna ya amfana da harajin VAT na kayan da aka batar a jiharsa.
Sannan Bukarti bai yarda akwai alkaluman da za su nuna yadda Arewa za ta ci moriyar harajin kayan da aka batar a jihohinta ba.
Talba ya yi magana kan kudirin haraji
Dazu labari ya zo cewa tsohon gwamnan Neja, Mu'azu Babangida Aliyu ya koka kan yadda ake samun masu sukar kudirin haraji a jahilce.
A wani taro, Dr. Mu'azu Babangida Aliyu ya ce akwai mutanen da suke sukar kudirin ba tare da sun karanta cikakken abin da ya kunsa ba.
Asali: Legit.ng