Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Halin da Ake Ciki game da Jita Jitar Bullar Annobar 'Korona'
- Gwamnatin Tarayya a Najeriya ta ƙaryata rade-radin cewa an samu bullar annobar Korona a kasar
- Ma'aikatar lafiya ta Tarayya ita ta bayyana da haka inda ta ce bincike ya tabbatar babu alamar cutar a Najeriya
- Wanann na zuwa ne bayan yadda wasu rahotanni cewa an samu bullar annobar nauyin XEC a fadin kasar a yau Asabar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan jita-jitar cewa an samu yaɗuwar annobar Korona zuwa Najeriya.
Ma’aikatar lafiya ta musanta labarin da ake yaɗawa kan bullar annobar a kasar da cewa labarin kanzon kurege ne.
Gwamnatin Tarayya ta magantu kan billar Korona
Daraktan hulda da jama'a na ma'aikatar, Mista Alaba Balogun shi ya tabbatar da haka a yau Asabar 7 ga watan Disambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Balogun ya ce ba a samu wata shaida na sabon nau’in cutar Korona mai suna XEC a Najeriya ba.
Har ila yau, ma’aikatar ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su kwantar da hankulansu tare da cigaba da bin ka’idojin tsafta na yau da kullum.
Yadda nau'in sabuwar annobar 'Korona' yake
Rahotanni sun ce nau’in Korona mai suna XEC ya kasance yana da ƙarfi fiye da sauran nau’o’in cutar, cewar Punch.
Bayanai sun tabbatar da cewa an fara samu a kasar Australia kuma ya bazu zuwa ƙasashe 29 na duniya baki daya.
Wannan ya tayar da hankula game da yadda zai iya shafar tsarin kiwon lafiya a fadin duniya.
Sai dai ma’aikatar ta jaddada cewa bincike mai zurfi da ta gudanar a iyakokin kasar da asibitoci ya nuna babu wata alamar wannan nau’in cutar a Najeriya.
An fadi yadda za ta kwato bashin Korona
Kun ji cewa yan Najeriya da dama sun samu bashin Gwamnatin Tarayya na miliyoyin kudi domin rage radadi a lokacin annobar Korona.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana yadda wadanda suka ci gajiyar shirin za su mayar da kudin, mutane da dama sun ki mayar da bashin kan lokaci.
Saboda haka gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar mayar da bashin cikin gaggawa ko kuma ta dauki wani mataki na daban.
Asali: Legit.ng