Hatsarin Mota Ya Katsewa Amarya da Ango Cin Amarci Bayan Samun Raunuka a Titin Legas

Hatsarin Mota Ya Katsewa Amarya da Ango Cin Amarci Bayan Samun Raunuka a Titin Legas

  • Hatsarin mota ya yiwa amarya da ango illa a wani yankin jihar Legas, inda mutane sama da 18 suka samu raunuka
  • Rahoto ya bayyana cewa, motar haya ce da karamar mota suka yi taho-mu-gama har ta kai ga samun mummunan rauni
  • Hukumomin tsaro sun yi kira mai karfi ga masu tuka ababen hawa da su kula wajen tafiyar da ayyukansu na yau da kullum a tituna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Legas - Wani hatsarin da afka da motocin haya guda biyu ya jikkata mutane 18, ciki har da wata sabuwar amarya da angonta a gadar Third Mainland da ke jihar Lagos ranar Asabar.

Mai magana da yawun Hukumar Kula da Zirganiyar Ababen Hawa ta Jihar Lagos (LASTMA), Adebayo Taofiq, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne yayin da wata motar bas kirar LT ta samu matsalar birki tana gudu, sannan ta bugi wata karamar mota a gefe.

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa sun tafka asara, wuta ta babbake miliyoyin Naira a Nasarawa

Yadda hatsarin mota ya raunata ango da amaryarsa
Hatsarin mota ya raunata amarya da ango a Legas | Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Yadda hatsarin ya auku tsakanin motoci biyu

Hatsarin ya jawo wa fasinjoji daban-daban raunuka masu tsanani, ciki har da karyewar wasu gabobi a jiki da dai sauran munanan raunuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Taofiq, karamar motar mai lamba AGL 22 YE da motar hayar mai lamba BFG 204 XF ne suka yi taho-mu-gama.

Ya ce:

“An samu nasarar ceto mutane 18 da suka samu raunuka daga hatsarin, ciki har da sabuwar amarya da ango da ke kan hanyarsu ta komawa gida daga ofishin rajistar aure da ke Ikoyi.”

Yadda aka kawo dauki ga fasinjoji

Ya kara da cewa fasinjoji 16 daga cikin motar hayar; mata 11 da maza 5, sun samu raunuka sosai kuma an garzaya da su zuwa Cibiyar Kula da Agajin Gaggawa ta Jihar Lagos da ke kusa da Toll Gate a kan babbar hanyar Lagos-Ibadan.

Mutane biyu daga cikin fasinjojin sun samu munanan raunuka sakamakon makalewa a cikin motar, kamar yadda jaridar Punch na naqalto.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun raunata mahaifiyar Gwamna da kanwarsa? Yan sanda sun yi martani

LASTMA tare da hadin gwiwar ma’aikatan agaji sun ciro su, sannan aka kai su asibitin Gbagada don karin kulawa mai kyau.

Sakon LASTMA ga wadanda suka yi hatsari

Shugaban LASTMA, Olalekan Bakare-Oki, ya jajantawa wadanda suka jikkata tare da yi masu fatan samun sauki cikin gaggawa.

Ya yi kira ga direbobi da su rika taka tsantsan a hanya, musamman wajen kula da lafiyar motoci da kaucewa gudu mai wuce kima.

Taofiq ya bayyana cewa aikin wayar da kan jama’a da LASTMA ke yi, musamman ta bangaren Tagawar Mata Jami’an Tsaro, na da nufin inganta tsaro a hanyoyin Lagos yayin bukukuwan karshen shekara.

Hukumomin agaji da suka halarci wurin sun hada da LASTMA, LASEMA, LASAMBUS, da ‘yan sanda don tabbatar da aikin ceto.

Hatsarin mota ya kashe amarya

A wani labarin na daban, kun ji yadda hatsarin mota ya yi sanadiyyar wata amarya yayin da ake ta bikin aurenta.

Kara karanta wannan

Rundunar sojoji ta cafke jami'anta saboda cin zarafin farar hula

Wannan lamari ya tada hankali, inda dangi da 'yan uwa da abokai suka shiga jimamin rashin amarya.

Ana yawan samun hadurran mota a Najeriya da ke kai wa ga mutuwar mutane a lokuta mabambanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.