Shugabannin Arewa Sun Nemo Mafita kan Kudirin Haraji, Ana Tattaunawa domin Kare Yankin

Shugabannin Arewa Sun Nemo Mafita kan Kudirin Haraji, Ana Tattaunawa domin Kare Yankin

  • Ana cigaba da kai ruwa rana a Majalisun Tarayya game da sabon kudirin haraji tsakanin yan Majalisun Arewa da Kudu
  • Majalisar Wakilai ta dakatar da tattaunawa kan kudirin harajin bayan yan majalisar daga Arewa sun kalubanci tsarin
  • Hakan ya biyo bayan ce-ce-ku-ce da ake ta yi kan sabon kudirin haraji musamman daga yankin Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Yayin da ake cigaba da korafe-korafe kan kudirin haraji, jagororin Arewa sun fara neman mafita.

Hakan ya biyo bayan kudirin haraji da yake ke kara rincabewa wanda ya fara kawo sabani a kasar tsakanin yankunan kasar.

Shugabannin Arewa sun fara tattaunawa kan kudirin haraji
Wasu yan Majalisa daga Arewa sun barranta da yan Kudu kan kudin haraji. Hoto: Sanata Barau I Jibrin.
Asali: Facebook

Kudirin haraji: Yan Arewa sun fara neman mafita

Vanguard ta ruwaito cewa jagororin Arewa na kokarin neman yadda za su yi gyara domin ganin kudirin bai cutar da yankin ba.

Kara karanta wannan

Arewa da Kudu: Yadda kudurin harajin Tinubu ya raba kan 'yan majalisa da manyan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu ‘yan majalisar dokoki daga Arewa na cigaba da gudanar da jerin taruka kan batun domin neman mafita.

A bangarenta, kungiyar League of Northern Democrats (LND) ta kaddamar da kwamiti na musamman domin tantance dokokin da aka gabatar.

Kwamitin zai nazarci batutuwan dokokin daya bayan daya saboda gano sassan da za su iya cutar da yankin Arewa.

Matsayar Sanatocin Kudu kan kudirin haraji

A halin yanzu, ‘yan majalisar dattawa daga yankin Kudu gaba ɗaya sun nuna goyon baya ga dokokin harajin.

Sai da takwarorinsau daga yankin Arewa mafi yawansu na adawa da matakin saboda wasu lamura a cikinsa.

Haka nan, yayin da Sanatoci ke ci gaba da tattaunawa kan dokokin, Majalisar Wakilai ta dakatar da shirin nazari kan batun kudirin haraji.

Hakan ya biyo bayan kin amincewa da kudirin da wasu yan Majalisa daga Arewa suka yi kan zargin cutar da Arewa.

Matasan Arewa sun goyi bayan Sanata Barau

Kara karanta wannan

Ma'adanai: Sojojin Nijar sun fatattaki babban kamfanin Faransa

Kun ji cewa wasu matasan Arewacin Najeriya sun bayyana rashin jin dadi yadda aka rika sukar matsayar Sanata Barau Jibrin.

Matasan da su ka yi magana a Katsina sun ce mataimakin shugaban majalisa ya yi rawar gani a kan batun kudirin haraji.

Sakataren kungiyar, Hamza Katsina ya shaida cewa Sanata Barau ya dauki matakan da su ka dace a halin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.