Naira Tana Ta Bada Mamaki, Dala Ta Cigaba da Karyewa a Kasuwar Canjin Kudi

Naira Tana Ta Bada Mamaki, Dala Ta Cigaba da Karyewa a Kasuwar Canjin Kudi

  • Kudin Najeriya watau Naira ya mike a kasuwar canji, ana sa ran ganin karshen karyewar da aka dade ana gani
  • A cikin watanni shida da suka gabata, kusan babu lokacin da aka saida Dalar Amurka a kan kasa da N1600
  • Masu sa ran Dala ta kara tashi sun rasa N10bn, Naira ta koma $1/N1500, ma’ana ta kara daraja da kusan N300

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Naira ta gamu da gagarumar nasara wanda ake ganin shi ne mafi girma a duk tsawon shekarar nan ta 2024 mai karewa.

A ‘yan kwanakin farkon Disamban nan, kudin Najeriyan ya tashi a kasuwannin canji da kuma bankuna a kan kimar dalar Amurka.

Naira
Darajar Naira ya tashi a kan Dala a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jaridar The Nation ta rahoto cewa an saida Dalar Amurka a kan N1, 515 a ranar Alhamis, kuma akwai yiwuwar Naira ta kara tashi.

Kara karanta wannan

TCN zai magance matsalolin wutar lantarki, an fara inganta manyan tashoshi 3

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan yana nufin darajar Naira ta karu da N200 daga N1, 715 da aka yi cinikin kudin.

Naira ta danne Dala a makon nan

Ranar Laraba, an saida kowace Dalar Amurka a kan N1, 695 yayin da mutane suka saye kudin wajen a kan N1, 725 ranar Talata.

An shafe kusan watanni shida ba a saida ko saye Dala a kan kasa da N1, 600 a Najeriya ba, har wasu sun fara fitar da tsammani.

A kasuwar canji, Naira ta tashi da 2.08% a shekaran jiya idan aka kamanta da farashin da aka saida Dala a yammacin ranar Laraba.

Meyasa Naira ta ke tashi a yanzu?

Bayanan da aka samu daga kafar NFEM sun nuna Dala karyewa ta ke yi, Business Day ta ce lamarin zai kai har farkon badi.

Watakila tsarin EFEMS wanda bankin CBN ya fito da shi ya yi tasiri wajen karyewar Naira.

Kara karanta wannan

Faduwar darajar Naira ya sake rikirkita komai, bashin Najeriya ya karu da N30trn

Masu nazarin tattalin arziki sun ce ‘yan canji sun yi asarar har N10bn a kan Dalar Amurka da suka ajiye saboda farfadowar Naira.

Akwai kaulin da ke nuna masu zuba hannun jari sun fara gamsuwa da yadda kasuwar ta ke tafiya bayan canjin tsarin da aka yi.

Karya Naira ya kara bashin Najeriya

Faduwar darajar Naira ya yi matukar tasiri kan ƙaruwar bashin da ake bin Najeriya kamar yadda rahoto ya nuna kwanan nan.

A cikin shekara guda kacal, bashin da yake kan wuyan Najeriya ya karu da fiye da N30trn saboda darajar Naira da CBN ya karya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng