‘Ku Kwantar da Hankalinku’: Sultan kan Kudirin Haraji bayan Ganawa da Ribadu
- Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA) ta yi kira ga al'umma da su kwantar da hankulansu kan kudirin haraji
- Majalisar karkashin shugabancin Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar ta ce sun yi ganawa kan kudirion kuma sun fahimci inda aka dosa
- Hakan ya biyo bayan ce-ce-ku-ce da ake ta yi kan sabon kudurin haraji da wasu ke ganin zai gurgunta tattalin arzikin kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA) ta kwantarwa yan kasa hankali kan sabon kudirin haraji.
Majalisar ta shawarci shugabannin siyasa su saukaka tashin hankali tare da kawo karshen rarrabuwar kawuna kan kudurin gyaran haraji.
Haraji: Sarkin Musulmi ya gana da Ribadu
Premium Times ta ce Majalisar ta bayyana cece-kucen da ake yi kan dokokin da aka gabatarwa Majalisar Dattawa ta kasa a matsayin mara amfani da hujja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan ganawar Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar da hadimin Bola Tionubu kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.
A cikin sanarwar da Sakataren Majalisar, Farfesa Salisu Shehu ya sanyawa hannu, NSCIA ta bukaci gudanar da shawarwari na tsanaki da tattaunawa mai ma’ana kan kudurin harajin.
Kudirin haraji: Sarkin Musulmi ya shawarci al'umma
Majalisar ta bukaci al’ummar Musulmi su kasance masu fatan alheri ga makomar kasa a kowane lokaci.
Haka kuma ta yi addu’a ga shugabanni da rokon Allah ya basu hikima wajen inganta rayuwar al’umma, cewar The Guardian.
Shugabannin Musulmi daga sassa daban-daban na kasar sun halarci taron ciki har da manyan malamai da ministoci da sauran shugabanni.
Matasan Arewa sun yabawa Sanata Barau
Kun ji cewa wasu matasan Arewacin kasar nan sun bayyana rashin jin dadin yadda aka rika sukar matsayar Sanata Barau Jibrin.
Matasan da su ka yi magana a jihar Katsina sun ce mataimakin shugaban majalisa ya yi rawar gani a kan batun kudirin haraji.
Sakataren kungiyar, Hamza Katsina ya shaida cewa Sanata Barau ya dauki matakan da su ka dace a halin da ake ciki a kasar.
Asali: Legit.ng