Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda, Sun Tura Miyagu da Dama Zuwa Barzahu
- Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro, sun samu nasara kan ƴan ta'adda a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma
- Jami'an tsaron sun kai samame kan maɓoyar ƴan ta'adda inda suka hallaka da dama daga cikinsu a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar
- Sojojin sun kuma ƙwato babura daga hannun ƴan ta'addan bayan sun ji wuta sun tsere zuwa cikin daji sakamakon artabun da aka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar kashe ƴan ta’adda da dama a jihar Zamfara.
Dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'addan ne a wani samame da suka kai maɓoyarsu a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda sojoji suka ragargaji ƴan ta'adda
Ya ce dakarun runduna ta 1 tare da haɗin gwiwar Operation Forest Yinzuya (OPFY) sun ƙaddamar da farmaki kan ƴan ta’addan ne a ranar Juma’a.
Masanin ya ce an kai harin ne a maɓoyar ƴan ta’addan ne biyo bayan samun bayanan sirri na tsawon makwanni kan harkokinsu a yankin.
Dakarun sojojin tare da tallafin sojojin sama sun yi artabu da ƴan ta’addan, wanda hakan ya yi sanadiyar kashe da dama daga cikinsu yayin da sauran suka tsere.
Sojojin sun kashe ƴan ta'adda da ba a tantance adadinsu ba a samamen, yayin da wasu kuma aka kai musu hari ta sama yayin da suke yunƙurin tserewa da shanu.
Sojojin sun ƙwato babura guda uku da ƴan ta’addan suka gudu suka bar su.
Sojoji sun ragargaji ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya sun yi ruwan bama bamai kan mafakar ƴan ta'adda a Rugan Mai Taru, da ke Arewacin ƙaramar hukumar Tsafe, a jihar Zamfara.
Ruwan bama bamai da jiragen sojojin suka yi, ya yi sanadiyyar hallaka ƴan ta'adda da dama tare da lalata kayayyakin tsaro a sansaninsu.
Asali: Legit.ng