Mutuwar El Mu’az: Malamin Addini Ya Tura Sakon Gargadi ga Kahutu Rarara
- Malamin Musulunci a jihar Kaduna Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria ya ba mawaki Dauda Kahutu Rarara shawara
- Malamin ya shawarci Rarara ya ji tsoron Allah kan abubuwan da yake yi musamman yin wakoki domin kawar da hankulan mutane
- Hakan na zuwa ne bayan fitaccen mawakin Kannywood, El-Muaz Birniwa ya rasu a daren ranar Alhamis, 5 ga watan Disambar 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Fitaccen malamain Musulunci, Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria ya magantu bayan mutuwar mawaki El-Muaz Birniwa.
Malamin ya ce mutuwar mawakin wa'azi ne ga mawaka musamman Dauda Kahutu Rarara kan abubuwan da yake yi.
Mutuwar El-Muaz: Shehin malami ya shawarci Rarara
Sheikh Alkali Salihu Zaria ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Abdullahin Gwandu TV ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehin malamin ya ce tabbas Rarara ba ya kyautawa saboda kullum aka shiga wahala sai ya yi waka domin kawar da hankulan mutane.
Malamin ya shawarci Rarara ya gaggauta tuba kafin haduwarsa da Allah domin mutuwar dan uwansa ya zama wa'azi a gare shi.
Malamin Musulunci ya soki Rarara kan wakokinsa
"Mutuwar El-Muaz izina ne ga sauran mawaka musamman Rarara ka ji tsoro Allah, al'umma suna shiga jarabawa a daida lokacin za ka yi waka domin ka kawar da hankulan mutane."
"Gun ga wadannan mawakan, halakakku ne yan iska suke binsu, al'umma su shiga bala'i ku ne za ku zo da wake na cutar da mutane."
"To ga dan uwanka El-Muaz ya amsa kiran Alla, Rarara ka gaggauta tuba wadannan abubuwa da kake yi ba za su fissheka ba."
"Me kake nema wanda Allah bai maka ba kudin ka yi, sunan ka yi, wakar ka iya amma muma talakawa sai ka cutar da mu."
- Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria
Fitaccen mawaki ya riga mu gidan gaskiya
Kun ji cewa Allah ya karbi rayuwar shahararren mawakin Hausa, El-Muaz Birniwa a daren ranar Alhamis, 5 ga watan Disambar 2024.
Abdul M Shareef, jarumi a masana'antar Kannywood ne ya sanar da rasuwar El'Mua'z tare da yin adduar Allah Sarki ya jikansa.
Asali: Legit.ng