'Yan Bindiga Sun Kai Harin Ban Mamaki, Sun Kashe Wata Yar Kasuwa da Malamin Addini
- Ƴan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun kashe wata ƴar kasuwa da limamin coci a Jalingo, babban birnin jihar Taraba
- Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce akwai abin mamaki a hare-haren
- Abdullahi Usman ya ce maharan sun shiga gidajen mutanen biyu, suka kashe su su ba tare da ɗaukar ko da allura ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Taraba - Wasu ‘yan bindiga sun kashe wata ‘yar kasuwa a unguwar Mayo Dasa da ke cikin Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da tsakar daren Juma’a 6 ga Disamba, 2024.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, Abdullahi Usman ya tabbatar da hakan ga Channels tv ta wayar tarho.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Miyagun 'yan bindiga sun kashe 'yar kasuwa
Jami'in ya ce a lokacin da ‘yan bindigar suka kutsa kai cikin gidan matar, sun yi amfani da adduna wajen karya tagar gidan.
Abdullahi Usman ya ce a bayanin da suka samu, maharan sun bindige matar tana tsakiyar karatun jarabawa, harsashin ya fasa ta bayanta ya ɓullo cikinta.
Kakakin ƴan sandan ya ce:
"Tana cikin karatu a ɗakinta a shirye-shiryen jarabawar da suka fara, ba zato ba tsammani maharan suka kutsa kai suka buɗe mata wuta.
"Sun harbe ta a baya harsashi ya shiga ya fito ta cikinta. Lokacin da suka fasa tagogin mutanen da ke zaune a gidan sun fito a tsorace amma abin mamakin ba su tafi da kowa ba.
Mai magana da yawun ƴan sandan ya kuma ƙara da cewa bincikensu ya nuna maharan ba su ɗauki komai ba a gidan, kashe matar kawai suka yi.
Ƴan bindiga sun hallaka malamin coci
Hari na biyu da aka kai a cewar kakakin ‘yan sandan ya faru ne a unguwar Jerbanbur da ke Jalingo.
Abdullahi Usman ya ce wasu ƴan bindigar sun buɗewa limamin coci wuta har ya mutu kuma ba su ɗauki ko da allura ba a gidan.
Ya ce waɗannan hare-haren abin mamaki ne da al'ajabi domin ƴan bindigar sun saba kisa, su sace mutane don neman kuɗin fansa, rahoton Daily Post.
Taraba: Maharan sun kashe manomi
A wani labarin, kun ji cewa ƴan bindiga sun kashe wani fitaccen manomi, sun sace wasu da dama a jihar Taraba da ke Arewa maso Gabas.
Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa ƴan bindiga sun buƙaci a ba su maƙudan kuɗin fansa kafin su saki manoman da suka sace.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng