Tinubu Ya ba Faransa Damar Kafa Sansanin Sojoji a Arewa? Rundunar Tsaro Ta Magantu

Tinubu Ya ba Faransa Damar Kafa Sansanin Sojoji a Arewa? Rundunar Tsaro Ta Magantu

  • Rundunar tsaro a Najeriya ta yi martani kan batun cewa Bola Tinubu ya yi yarjejeniya da Faransa kan kawo sojojinta Najeriya
  • Hafsan tsaron kasar, Janar Christopher Musa ya musanta labarin da ake ta yaɗawa kan kafa sansanin sojoji musamman a Arewa
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake jita-jitar Tinubu ya hada baki da Faransa domin kafa sansanin sojoji da hadin guiwa kan hakar ma'adinai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya yi magana kan rade-radin kawo sojojin Faransa kasar.

Janar Christopher Musa ya karyata rahotannin da ke cewa an ba Faransa izinin kafa sansanin sojojin kasashen waje a Najeriya.

Rundunar tsaro ta yi martani kan jita-jitar kawo sojojin Faransa Najeriya
Hafsan tsaro, Janar Christopher Musa ya musanta zargin kawo sojojin Faransa Najeriya. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Hafsan tsaro ya magantu kan kawo sojojin Faransa

Hafsan tsaron ya yi watsi da jita-jitar inda ya ce a ziyarar da Bola Tinubu ya yi ya sanya hannu kan yarjejeniyoyi da dama, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Ma'adanai: Sojojin Nijar sun fatattaki babban kamfanin Faransa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Janar Musa ya ce babu zancen hadin guiwa da amincewa da kafa sansanin sojojin kasashen waje a Najeriya.

A cewarsa, babu wata ƙungiyar ƙasashen waje da za ta iya kafa sansanin sojoji a Najeriya ko a Arewa ko a ko’ina cikin ƙasar.

Hafsan tsaro ya magantu kan yarjejeniyar Tinubu

“Shugaban kasa ya bayyana hakan a fili, duk wani abu da ya sanya hannu a kai yarjejeniya ce ta hadin guiwa kan cinikayya da al’adu da tattalin arziki."
“Babu wani abu makamancin haka, shugaban kasa ya fahimci muhimmancin kare ƙasar nan kuma ba zai taɓa bari wata ƙungiyar ƙasashen waje ta kafa sansani a Najeriya ba."

- Janar Christopher Musa

Sheikh Asada ya magantu kan jawo sojojin Faransa

Kun ji cewa yayin da ake ta magana kan sabon kudirin haraji, malamin Musulunci ya ce akwai masifar da ake tunkara da ta fi wannan a cewarsa.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu ya yarje tare da gayyato kasar Faransa ta tona ma'adanai a Najeriya

Sheikh Murtala Bello Asada ya ce alakar Bola Tinubu da kasar Faransa ba karamar fitina za ta jawo ba, musamman a jihar Sokoto.

Malamin ya nuna damuwa kan yadda ake shirin kawo sojojin Faransa saboda hadin guiwa, ana tsoron dakarun za su shigo har Sokoto.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.