Sanusi II Ya Yi Martani yayin da Jami'an Tsaro Suka Mamaye Fadar Sarkin Kano

Sanusi II Ya Yi Martani yayin da Jami'an Tsaro Suka Mamaye Fadar Sarkin Kano

  • Jami’an tsaro sun mamaye fadar Sarki Muhammadu Sanusi II da ke Ƙofar Kudu, lamarin da ya jefa mazauna Kano cikin rudani
  • Sarki Sanusi II yayin hudubar Sallar Juma'a ya yi martani kan wannan mamayar inda ya ce wasu ne ke neman tayar da fitina
  • Mai martaban ya yi kira ga mazauna Kano da su guji rikici, yana mai cewa haƙuri shi ne mafita ga duk wata fitina da ake ƙoƙarin tayarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi martani yayin da jami'an tsaro suka mamaye fadar sarkin Kano da ke Ƙofar Kudu.

Da safiyar Juma’a, mazauna Kano suka wayi gari da ganin tarin jami’an tsaro a fadar Sarki Muhammadu Sanusi II, lamarin da ya jefa su a dari dari.

Sanusi II ya yi magana yayin da jami'an tsaro suka mamaye fadar sarkin Kano
Sanusi ya nemi mazauna Kano da su guji fitina yayin da jami'an tsaro suka mamaye gidan sarki. Hoto: @masarautarkano/X, BBC
Asali: UGC

Abin da ya faru a fadar sarkin Kano

Kara karanta wannan

Yadda Sanusi II ya yi zaman fada duk da jibge jami'an tsaro a gidan Sarkin Kano

Rahoton BBC Hausa ya nuna cewa ba a taɓa ganin yawan jami’an tsaro a fadar sarkin Kano ba kamar wannan lokaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’an tsaron da aka jibge sun haɗa da masu ɗauke da makamai yayin da aka jibge motocin tarwatsa masu zanga-zanga domin jiran ko ta kwana.

Tun farko, an shirya cewa Sarki Sanusi II zai raka Wamban Kano, Mannir Sanusi, zuwa masarautar Bichi domin kama aiki a matsayin hakimi.

To sai dai kuma, jibgewar jami’an tsaron ya kawo cikas ga wannan shiri na tafiyar Mannir Sanusi zuwa fadar Bichi.

Abin da Sarki Sanusi II ya ce game da lamarin

Kamar yadda aka saba, Sarki Muhammadu Sanusi II ya jagoranci sallar Juma’a a babban masallacin birnin Kano, inda ya gabatar da huɗuba mai jan hankali.

A cikin huɗubarsa, sarkin ya buƙaci mazauna Kano da su kwantar da hankalinsu tare da guje wa duk wata fitina, yana mai cewa haƙuri shi ne mafita.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun rufe kofar shiga kofar fadar Sarkin Bichi, an dage nada hakimi a Kano

A cewarsa abubuwan da ake gani a kwanakin nan suna nuni da cewa wasu na shirin haifar da rikici da zubar da jini a Kano, kuma ba wannan ne karon farko ba.

Sarkin ya ce ana ƙoƙarin fusata jama’a su ɗauki doka a hannunsu, amma ya roƙi al'ummar Kano da su guji faɗawa wannan tarkon.

"Duk mutumin da ya kawo fitina a Kano, zuwa zai yi ya tafi, dukiyarmu za a ƙona. A daure a yi haƙuri, haƙuri ba tsoro ba ne, a yi addu'a."

- A cewar Sarki Sanusi II.

Gwamnatin Kano kan mamaye fadar Sarki

A wani lanarin mun ruwaito cewa gwamnatin Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta ce ta yi mamakin yadda jami’an tsaro suka mamaye fadar Sarki.

Sakataren gwamnatin Kano Abdullahi Baffa Bichi ya bayyana cewa babu wani abu na fargaba ko tashin hankali a jihar Kano, kuma mamayar ba za ta yi tasiri ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.