Ana cikin Rigimar Sarauta, Sanata Kashim Shettima Ya Dira Jihar Kano a Yau Juma'a
- Rahotanni sun tabbatar da cewa mai girma mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya isa jihar Kano a yau Juma'a 6 ga watan Disambar 2024
- Kashim Shettima ya dira a Kano domin kai ziyara sashen kamfanoni da ke Challawa da kuma rukunin kamfanin Mamuda
- Wannan ziyara ta Kashim na zuwa ne yayin da rigimar sarauta ta dawo sabuwa a yau Juma'a 6 ga watan Disambar 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya sauka a jihar Kano da ta yi fice wajen kasuwanci.
Kashim Shettima ya isa Kano ne a yau Juma'a 6 ga watan Disambar 2024 domin duba wasu ayyuka musamman a rukunin kamfanoni da ke Challawa.
Kashim Shettima ya dauka a jihar Kano
Wannan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da Abubakar Sadik Kurbe ya wallafa a shafinsa na X a yammacin yau Juma'a 6 ga watan Disambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce Shettima ya shiga Kano ne domin ziyara rukunin kamfanin Mamuda tare da kuma ganawa da shugabanninsa.
Har ila yau, Shettima zai kuma yi duba game da ayyukan kamfanin musamman wurin samar kayayyaki da tace ruwa.
Himmatuwar gwamnatin Tinubu wurin inganta masana'antu
Rahotanni sun tabbatar da cewa ziyarar Shettima na da alaka da himmatuwar gwamnatin Bola Tinubu wurin inganta masana'antu a Najeriya.
Har ila yau, masu ruwa da tsaki suna ganin hakan zai kara inganta kamfanoni a jihar da kuma samar da ayyukan yi ga matasa duba da tasirin masana'antu a ƙasar.
Kalli faifan bidiyon a kasa:
Kashim Shettima ya dauko hanyar gyara lantarki
Kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya jagoranci taron majalisar tattalin arziki a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.
A yayin taron, majalisar tattalin arzikin ta amince da kafa kwamitin da zai yi aiki domin samar da wutar lantarki a kasar nan.
Kashim Shettima ya yi karin haske kan ayyukan da kwamitin zai yi yayin da ya ce samar da wuta hakki ne na al'umma ba gata ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng