Ana Tsaka da Rigimar Sarauta a Kano, Kotu Ta Yi Hukunci kan Dakatar da Muhuyi Magaji
- Kotun Daukaka Kara a Abuja ta wanke shugaban hukumar hukumar karɓar korafe-korafe da rashawa a Kano, Muhuyi Magaji Rimingado
- Kotun ta ce kwata-kwata matakin da kotun da'ar ma'aikata ta CCT ta yi ya saba ka'ida kuma bai inganta ba
- Wannan na zuwa ne bayan dakatar da Muhuyi Magaji a ranar 4 ga Afrilun 2024 sakamakon zarge-zargen da hukumar CCB ta yi masa kan rashin da’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta rushe dakatarwar da aka yi wa shugaban hukumar karɓar korafe-korafe da rashawa a Kano, Muhuyi Magaji Rimingado.
Hukuncin ya biyo bayan yanke shawarar wani kwamitin alkalai uku, karkashin jagorancin Mai Shari’a Umaru Fadawu.
Dakatar da Muhuyi Rimingado daga muƙaminsa
Channels TV ta ruwaito cewa kotun ta bayyana dakatarwar da kotun da'ar ma’aikata (CCT) ta yi a matsayin rashin adalci da tauye hakkokin Rimingado.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An dakatar da Muhuyi Magaji a ranar 4 ga Afrilun 2024 sakamakon zarge-zargen da hukumar da'ar ma'aikata (CCB) ta yi masa kan rashin da’a.
Alƙalin da ya yanke hukuncin, Danladi Umar a wancan lokaci ya shawarci Abba Kabir da sakataren gwamnatinsa su nada sabon shugaban hukumar.
Umar ya ce nada mukaddashin shugaban hukumar zai ba da damar kammala bincike kan zarge-zargen da ake yi wa Rimingado.
Kotu ta wanke Rimingado kan dakatar da shi
Sai dai Mai Shari’a Fadawu ya ce matakin da CCT da dauka bai inganta ba kuma ya sabawa ka'idojin adalci, cewar Tribune.
“Dakatarwar da CCT ta yi bai inganta ba kuma ya sabawa ka’idojin adalci na sauraron shari’a."
"Mun kuma bayar da umarnin cewa a sake tura shari’ar zuwa wani kwamitin daban na kotun.”
- Umaru Fadawu
Kotu ta bukaci korar Rimingado daga muƙaminsa
A baya, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta yi zama kan tuhume-tuhume da ke kan Muhuyi Magaji Rimingado.
Kotun ta umarci sallamar shugaban hukumar karɓar korafe-korafe da rashawa a Kano saboda saba umarnin kotu da ya yi bayan kararsa da ake kai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng