Gwamnan Arewa da Aka Ce Ƴan Bindiga Sun Farmaka Ya Sa DSS Sun Cafke 'Dan Jarida

Gwamnan Arewa da Aka Ce Ƴan Bindiga Sun Farmaka Ya Sa DSS Sun Cafke 'Dan Jarida

  • DSS ta kama Mustapha Bina bisa rahoton harin ‘yan bindiga kan tawagar gwamnan Neja da aka yada a rediyon Prestige FM Minna
  • Shugabannin kungiyar NUJ sun yi ƙoƙarin ganin DSS ta saki ɗan jaridar, wanda aka ce gwamna ya bada umarnin a cafke shi
  • Gidan rediyon ya nemi afuwa daga gwamnatin Neja kan rahoton, inda ta bayyana cewa an samu kuskuren tsari a ɗaukar labarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama Mustapha Bina, wani ɗan jarida mai aiki da jaridar People’s Daily a Jihar Neja.

An kama shi ne bayan ya bada rahoto kan harin ‘yan bindiga da aka ce sun kai wa tawagar Gwamna Muhammed Umaru Bago a Mashegu.

Gwamna ya sa DSS sun cafke dan jaridar da ya fitar da rahoton harin da aka kaiwa tawagarsa
DSS sun cafke dan jaridar da ya ce 'yan bindiga sun kaiwa gwamnan Neja hari. Hoto: @HonBago
Asali: Facebook

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto cewa an dauki wannan labarin a gidan rediyon Prestige FM Minna, inda Mustapha Bina ke aiki.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin ban mamaki, sun kashe wata ƴar Kasuwa da malamin addini

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Neja ya sa DSS ta cafke dan jarida

Wani ma'aikacin DSS ya ce kama Bina ya biyo bayan umarnin gwamna, saboda fushinsa kan yada rahoton da ya ɓata masa suna.

Shugaban NUJ na jihar, Abu Nmodu, da wasu shugabanni sun shiga tsakani, inda suka roƙi DSS da su saki ɗan jaridar.

Rahoton ya nuna cewa Mustapha Bina ya kwashe awanni a ofishin DSS kafin a bayar da belinsa bayan roƙon shugabannin NUJ.

Gidan rediyo ya nemi afuwar gwamna

Wani ma’aikacin DSS ya bayyana cewa kama ɗan jaridar zai iya ƙara dagula lamarin, don haka suka amince su sake shi a cewar rahoton SaharaReporters.

Duk da haka, kakakin gwamna, Bologi Ibrahim, da kwamishiniyar yaɗa labarai, Binta Mamman, sun musanta aukuwar harin a wata sanarwa.

Manajan daraktan Prestige FM, Zubair AbdulRauf, ya nemi afuwa daga gwamnatin jihar, yana mai amincewa an samu matsala a rahoton da suka yada.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi martani da jami'an tsaro suka kewaye fadar Sarki Sanusi II

'Yan bindiga sun farmaki gwamnan Neja?

Tun da fari, mun ruwaito cewa gwamnatin Neja ta karyata rahotannin da ake yaɗawa cewa wasu ƴan bindiga sun farmaki tawagar Gwamna Umaru Bago.

Sakataren yada labaran gwamnatin jihar, Bologi Ibrahim ya ce ayarin gwamnan na ci gaba da rangadin ayyuka a Neja ta Arewa ba tare da wata barazana ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.