'Yan Sanda Sun Rufe Kofar Shiga Kofar Fadar Sarkin Bichi, An Dage Nada Hakimi a Kano

'Yan Sanda Sun Rufe Kofar Shiga Kofar Fadar Sarkin Bichi, An Dage Nada Hakimi a Kano

  • Rundunar 'yan sandan Kano ta rufe kofar shiga fadar Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero a ranar Juma'a
  • Lamarin ya biyo bayan shirin da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ke yi na nada sabon hakimin Bichi a wannan rana
  • Haka kuma jami'an tsaron sun rufe kofar shiga fadar Sarkin Kano bayan an samu labarin zai raka sabon hakimin fadarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Rundunar ‘ yan sandan kasar nan ta cigaba da daukar matakai a rikicin masarautar Kano da ya kara kamari a yau Juma’a.

Bayan jami’ai da aka ajiye a gidan Sarki Muhammadu Sanusi II tun da sanyin safiyar yau, an kara tura jami’a kofar fadar Sarkin Bichi.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi martani yayin da jami'an tsaro suka mamaye fadar sarkin Kano

Bichi
An jibge jami'an tsaro a masarautar Bichi Hoto: Sani Bello Bature
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa rundunar ‘yan sandan kasar nan ta rufe kofar shiga fadar Sarkin Bichi ne a lokacin da ake dakon isowar sabon hakimin yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan sanda sun kori jama’a a fadar Bichi

Jami’an rundunar ‘yan sandan kasar nan sun kori dukkanin masu unguwanni da sauran sarakan da su ka taru a fadar Sarkin Bichi domin tarbar sabon hakimin da aka nada.

Wannan na zuwa ne bayan jibge ‘yan sandan a gaban gidan sarki Muhammadu Sanusi ya hana shi fita zuwa Bichi domin raka sabon hakimin da ya nada.

Kano: An daga bikin tarbar hakimin Bichi

Gwamnatin jihar Kano ta dage ranar tarbar sabon hakimin Bichi bayan jige jami’an tsaro da aka yi a fadar Sarkin Kano 16 da ta Sarkin Bichi a yau.

Wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na yankin, Tasi’u Jibo Dawanau ce ta bayyana haka, tare da bukatar jama’a su kwantar da hankalinsu, a kuma cigaba da harkoki.

Kara karanta wannan

Yadda Sanusi II ya yi zaman fada duk da jibge jami'an tsaro a gidan Sarkin Kano

Gwamnati ta yi martani kan mamaye fadar Sarki

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sakataren gwamnatin Kano, Abdullahi Baffa Bichi ya bayyana takaicin gwamnati bisa yadda jami'an tsaro su ka mamaye fadar Sarki.

Martanin ya zo ne bayan jami'an tsaro sun mamaye fadar Sarkin Kano 16, Malam Muhammadu Sanusi II a yayin da ake shirin nada sabon hakimin Bichi a yau.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.