Za a yi Aikin Sama da Naira Tiriliyan 4 a Masarautar Arewa da Ta Nada Tinubu Jagaba

Za a yi Aikin Sama da Naira Tiriliyan 4 a Masarautar Arewa da Ta Nada Tinubu Jagaba

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janyo saka hannun jarin $2.5 biliyan daga wani kamfani na kasar Brazil domin inganta noma a masarautar Borgu
  • Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya bayyana cewa za a yi amfani da filin hekta miliyan 1.2 domin samar da wuraren kiwo da noma
  • Yayin ziyara garin, gwamnan na Neja ya ba da gudunmawar Naira miliyan 100 ga kungiyoyin mata na Borgu domin karfafa tattalin arzikin su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Niger - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu wanda ke da sarautar Jagaban a Borgu ya jawo muhimmin aiki masarautar.

Bola Tinubu ya jawo saka hannun jarin $2.5bn wanda ya haura Naira tiriliyan hudu daga kamfani a kasar Brazil domin inganta kiwo, noman shinkafa da masara a Masarautar Borgu.

Kara karanta wannan

"Kudirin haraji ya bankado gazawar Arewa," Tsohon dan takarar shugaban kasa ya magantu

Tinubu
Tinubu ya jawo babban aiki a masarautar da ta nada shi Jagaba. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Hadimin gwamnan, Ibrahim Bologi ya wallafa a Facebook cewa gwamna Mohammed Umaru Bago ya bayyana haka ne yayin ziyara masarautar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bago ya bayyana cewa za a yi amfani da fili hekta miliyan 1.2 da ke kusa da hanyar Sokoto-Badagry domin aikin.

Gwamnan ya ce wannan mataki ya nuna yadda shugaba Tinubu ke kula da ci gaban masarautar Borgu da jihar baki daya.

Tattalin Borgu zai bunkasa inji gwamna Bago

A cewar gwamna Bago, wannan hannun jarin zai taimaka wajen kirkirar gonaki na zamani tare da kara habaka tattalin arziki da samar da aikin yi ga jama’ar masarautar Borgu.

Gwamna Bago ya yi kira ga jama’ar masarautar da su ci gaba da mara wa gwamnati mai mulki ta APC baya domin samun cigaba mai dorewa da zai kyautata rayuwar su.

Gwamna Bago ya ba mata tallafin kudi a Neja

Mohammed Umaru Bago ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 ga kungiyoyin mata na Borgu domin karfafa tattalin arzikin su da kuma basu damar dogaro da kai.

Kara karanta wannan

Sanusi II na shirin fita zuwa Bichi, jami'an tsaro sun mamaye fadar sarkin Kano

Haka zalika, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da ayyukan raya kasa da za su amfani al’ummar jihar Neja.

Gwamna Bago ya raba miliyoyi ga mata

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Neja ta raba Naira miliyan 250 ga kungiyoyin mata domin bunkasa kananan sana'o'i a Kontagora

Gwamna Umaru Bago ya ce zai cigaba da raba tallafi ga mata domin su zama masu dogaro da kai da gina tattalin arziki a jihar Neja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng