Matasan Arewa Sun Bayyana Kokarin Barau Jibrin wajen Dakatar da Kudirin Tinubu a Majalisa
- Wasu matasan Arewacin kasar nan sun bayyana rashin jin dadin yadda aka rika sukar matsayar Sanata Barau Jibrin
- Matasan da su ka yi magana a Katsina, sun ce mataimakin shugaban majalisa ya yi rawar gani a kan batun kudirin haraji
- Sakataren kungiyar, Hamza Katsina, ya shaida cewa Sanata Barau ya dauki matakan da su ka dace a halin da ake ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Wasu matasan Arewacin kasar nan sun bayyana jin dadin yadda mataimakin shugaban majalisa, Barau I Jibrin ya taka rawa a kan kudirin haraji.
Kungiyar 'Concerned Northern Group for National Unity and Integration' ta shaida cewa matakin da Barau I Jibrin ya dauka, ya nuna dattako.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Sakataren kungiyar, Hamza Katsina ya shaida cewa abin da Barayi ya yi, manuniya a kan kudirinsa ya tabbatar da adalci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barau: Matasa sun yabi mataimakin shugaban majalisa
Kungiyar matasan Arewa sun ce daukar matakin dakatar da tattauna kudirin harajin Tinubu da kafa kwamiti da zai sake duba batun, ya nuna dattakon Barau I Jibrin.
Bayan a sha sukar goyon bayan da kudirin da gwamnati ta bijiro da shi, mataimakin shugaban majalisar, ya ce an kafa kwamitin da zai duba batun.
An soki masu caccakar mataimakin shugaban majalisa
Kungiyar matasan Arewacin kasar ta soki lamarin masu kokarin siyasantar da batun kudirin haraji da yadda Barau I Jibrin ya yi magana a kan batun.
Hamza Katsina ya ce:
"Abin takaici ne ganin yan siyasa da kungiyoyin masu ruwa da tsaki suna gaggauta yin hukunci kan shugabannin Arewa da suka yi kokari matuka don kare muradun yankin,"
Mataimakin shugaban majalisa, Barau ya sha suka
A wani labarin, mun ruwaito cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I Jibrin ya fuskanci kalubale a Arewacin kasar nan bisa goyon bayan kudirin haraji.
Mazauna shiyyar Arewa, ciki har da malamai da masu amfani da kafafen sada zumunta sun zargi Barau I Jibrin da rashin kishin muradun jama'ar da ya ke wakilta a majalisa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng