'Ana Shirin Markaɗe Mu': Malamin Addini Ya Hango 'Makircin' da Ake Kullawa Arewa

'Ana Shirin Markaɗe Mu': Malamin Addini Ya Hango 'Makircin' da Ake Kullawa Arewa

  • Ustaz Abubakar Salihu Zaria ya yi ikirarin cewa ana shirin 'markade' Arewacin Najeriya, yana mai kiran mutane su koma ga Allah
  • A cewar malamin, shirin da ake yi na kafa barikin sojojin Faransa a wani sharri ne da ake kullawa Arewa da ya wuce misali
  • Yayin da ya soki shugaba Bola Tinubu kan yarjejeniyarsa da Faransa, Ustaz Salihu ya yi gargadin cewa Arewa ba ta bukatar barikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Babban malamin addinin Musulunci, Alkali Ustaz Abubakar Salihu Zaria ya yi ikirarin cewa ana kulla makirci domin 'markade' Arewacin Najeriya.

Ustaz Salihu Zaria ya ce da 'yan Arewa sun san irin sharrin da ake kullawa yankin da sun daina bacci, sun koma masallatai suna rokon Allah.

Ustaz Abubakar Salihu Zaria ya yi magana kan yarjejeniyar Tinubu da Faransa
Ustaz Abubakar Salihu Zaria ya ce ana kullawa Arewacin Najeriya wani babban makirci. Hoto: Alkali Ustaz Abubakar Salihu Zaria, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

"Ana kullawa Arewa sharri" - Alkali Abubakar Salihu Zaria

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun bayyana kokarin Barau wajen dakatar da kudirin Tinubu a Majalisa

A wani faifan bidiyo da ya yadu a kafofin sada zumunta, wanda Legit Hausa ta gani a shafin Mubarakh Sani na Facebook, an ji malamin na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wallahi jama'a, in kuka san sharrin da ake kullawa Arewacin Najeriya na shirin markade mu, da dukkaninmu mun daina bacci, mun dawo masallaci mun tarewa Allah."

Ustaz Abubakar Salihu Zaria ya yi nuni da cewa kasashen Afrika da dama sun yanke alakarsu da kasar Faransa, saboda wasu dalilai na abin da kasashen ba su yarda da shi ba.

Sai dai kuma malamin ya zargi shugaban kasa Bola Tinubu da zumudin kulla yarjejeniya da Faransa ba tare la'akari da abin da ka iya zuwa ya dawo ba.

Malami ya soki Tinubu kan alakarsa da Faransa

Fitaccen malamin addinin ya soki shugaban kasar kan yarjejeniyar da ya yi ikirarin ya cimmawa da Faransa ta kafa barikin sojoji a Arewa, inda ya yi ikirarin cewa:

Kara karanta wannan

TCN zai magance matsalolin wutar lantarki, an fara inganta manyan tashoshi 3

"Ya je ya sako mana hannu, za a zo a samu wani yanki daga cikin yankinmu na Arewa, ko Sokoto ko Zamfara ko Kebbi, wai za ayi barikin sojoji na Faransa.
"To mu sojojin namu na Najeriya ma basu samu wadatacciyar bariki ba ballantana a gayyato mana wata kasa. Saboda haka mu bamu da bukata."

Malamin ya ce idan kuwa har gwamnatin tarayyar ta dage sai ta shigo da sojojin Faransa kasar nan, to sai dai a sauke su a can Legas, domin can ne mutane suka fi yawa.

Kalli bidiyon a nan kasa:

Malami ya hango matsala gaban Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa Primate Ayodele, shugaban Cocin INRI Spiritual, ya ce Najeriya za ta fuskanci hauhawar farashi mai tsanani a 2025

Malamin addinin ya ce hauhawar farashi a yanzu ba komai ba ne idan aka kwatanta da abin da ke tafe, inda ya bukaci gwamnati ta dauki matakin gaggawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.