Zanga Zangar Tsofaffin Sojoji Ta Haifar da Ɗa Mai Ido, Gwamnati Ta Fara Biyan Bukatunsu

Zanga Zangar Tsofaffin Sojoji Ta Haifar da Ɗa Mai Ido, Gwamnati Ta Fara Biyan Bukatunsu

  • Tsofaffin sojojin kasar nan sun fara samun hakkokinsu bayan sun gudanar da zanga-zanga ta kwanaki biyu a Abuja
  • Tsofaffin dakarun sun gudanar da zanga zanga ta kwanaki biyu domin tuna wa gwamnati ta rike hakkokinsu da ta yi
  • A sanarwar da ya fitar, karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya ce Bola Tinubu ya amince da fara biyan hakkokin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta fara waiwayar bukatun tsofaffin sojojin kasar nan da su ka kammala aiki bayan sun gudanar da zanga-zanga.

Karamin Ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle ne ya bayyana cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da a fara biyan tsofaffin dakarun hakkokinsu.

Sojoji
Gwamnati ta fara biyan sojoji hakkokinsu Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin sanarwar da daraktan hulda da jama’a na ma’aikatar tsaro, Henshaw Ogubike ya fitar a Abuja.

Kara karanta wannan

Atiku ya dura a kan 'yan sanda, ya soki yadda aka kama mai adawa da gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fara biyan tsofaffin sojoji hakkokinsu

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince a fara biyan tsofaffin sojoji kudadensu na fansho da sauran hakkokinsu.

Haka kuma za a biya karin albashi ga tsofaffin dakarun tsaron na watanni uku da sauran kudin da su ke bin gwamnatin tarayya.

An yabi Tinubu kan hakkokin sojoji masu ritaya

Karamin Ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle ya yaba wa shugaba Tinubu bisa gaggauta biyan tsofaffin sojoji hakkokinsu.

Ma'aikatar harakokin tsaro ta kasar nan, ta bayyana cewa an fara biyan tsofaffin jami'an tsaron hakkokinsu bayan sun gudanar da zanga zanga ta kwanaki biyu.

Tsofaffin sojoji sun yi zanga zanga a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu daga cikin tsofaffin sojojin kasar nan sun mamaye ma'aikatar kudi da ke Abuja domin bayyana kokensu kan hana su hakkokinsu.

Tsofaffin sojojin da su ka yi ritaya, sun nuna damuwarsu a kan yadda gwamnati ta rike karin albashinsu da wasu alawus-alawus da su ka bayyana cewa ya dace su samu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.