Tsofaffin sojoji da su ka zama sarakuna a Arewa
– A da can ‘yan gidan sarauta sun rika shiga aikin soji
– Irin su Janar Hassan Katsina ‘yan gidan sarauta ne
– An samu wasu daga ciki da su ka koma rawani bayan ajiye khaki
Legit.ng ke cewa a zamanin da can ‘Yan gidan Sarauta sun rika shiga aikin Soji wanda ake gani da martaba. An kuma dace an samu wasu daga ciki da su ka koma rataya rawani bayan sun ajiye khakin Soji.
A wani nazari da Jaridar Daily Trust tayi ta kawo da dama daga ciki, mun tsakayo wasu a nan:
1. Alhaji Sa’ad Abubakar III
Mai alfarma Sarkin Musulmi Soji ne asalin sa wanda ya kai har matsayin Janar. Birgediya-Janar ya ajiye aiki ne a shekarar 2006, bayan nan ya gaji sarutar gidan su ya zama Sultan na Sokoto.
KU KARANTA: An damke wani Dan ta'adda Dan Najeriya
2. Alhaji Muhammad Sami Sani
Mai martaba Sarkin Zuru babban ya shiga gidan Soja, wanda har ya rike mukamai ma da dama irin su GOC. Tsohon Manjo-Janar din ya koma rike da Sarautar Zuru.
3. Alhaji Garba Muhammad
Alhaji Garba mai girma Sarkin Lere ya gaji Dan uwan sa bayan ya rasu shekaru 6 da suka wuce. Sarkin tsohon Birgediya Janar na Soja ne wanda har ya taba rike Gwamnan Jihar Sokoto.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Jawabin Sarkin Kano kwanaki a Kaduna
Asali: Legit.ng