Yadda Gwamnoni 12 na Arewacin Najeriya Suka Kashe Naira Biliyan 700 a Watanni 9

Yadda Gwamnoni 12 na Arewacin Najeriya Suka Kashe Naira Biliyan 700 a Watanni 9

Gwamnonin jihohi 12 na Arewacin Najeriya sun kashe N698.87bn a kan kudaden gudanarwa, ciki har da abinci, tafiye tafiye, kayan aiki da sauransu a cikin watanni tara na farkon 2024.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

An kuma rahoto cewa wadannan jihohi sun samu N205.63bn ne kacal amma sun aro kusan ninki biyu na wannan adadi daga masu ba da lamuni na gida da waje.

Gwamnoni 12 na Arewacin Najeriya sun kashe N700bn a cikin watanni 9
Rahoto ya yi bayanin yadda gwamnoni 12 na Arewa suka kashe N700bn a wata 9 na 2024. Hoto: @CalebMutfwang, @SenBalaMohammed, @dikko_radda
Asali: Twitter

Wannan yana zuwa ne duk da karin kashi 40 cikin dari na kudaden da ake ware wa jihohin daga asusun tarayya, kamar yadda jaridar The Punch ta rahoto.

Wannan rahoto ya yi bayanin kudaden da jihohin Adamawa, Bauchi, Jigawa, Katsina, Kebbi, Kogi, Nasarawa, Neja, Filato, Taraba, Yobe da Zamfara suka batar a watanni tara na 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihohi 12 sun kashe N699.87bn wajen gudanarwa

Kara karanta wannan

Hajjin 2023: NAHCON ta mayarwa Alhazan Kebbi ₦301.56m saboda abin da aka yi masu

Jimillar kudaden gudanarwa da jihohin 12 suka kashe a watanni tara na farkon 2024 ya kai N699.87bn. Ga abin da kowace jiha ta kashe:

  • Adamawa: N41.45bn
  • Bauchi: N99.31bn
  • Jigawa: N35.69bn
  • Katsina: N40.73bn
  • Kebbi: N22.42bn
  • Kogi: N84.48bn
  • Nasarawa: N42.63bn
  • Niger: N41.28bn
  • Filato: N144.86bn
  • Taraba: N58.39bn
  • Yobe: N51.29bn
  • Zamfara: N36.34bn

N207.57bn aka samu a matsayin kudaden shiga

Jimillar kudaden shiga da jihohin suka tara ya kai N207.57bn, wanda bai kai ko da rabin kudin gudanarwar da suka kashe ba.

Ga abin da kowace jiha ta tara:

  • Adamawa: N9.16bn
  • Bauchi: N15.92bn
  • Jigawa: N18.41bn
  • Katsina: N29.95bn
  • Kebbi: N7.86bn
  • Kogi: N19.86bn
  • Nasarawa: N22.78bn
  • Niger: N29.22bn
  • Filato: N18.03bn
  • Taraba: N7.84bn
  • Yobe: N8.14bn
  • Zamfara: N18.46bn

Bashin da jihohi 7 suka karba

Jimillar basussukan da jihohi 7 cikin 12 suka karba ya kai N246.17bn, inda jihohin Katsina, Taraba, da Kogi suka karbi mafi yawa:

  1. Adamawa: N10.00bn
  2. Bauchi: N33.64bn
  3. Jigawa: N0.74bn
  4. Katsina: N72.89bn
  5. Kebbi: N24.59bn
  6. Kogi: N51.68bn
  7. Taraba: N52.63bn

Kara karanta wannan

TCN zai magance matsalolin wutar lantarki, an fara inganta manyan tashoshi 3

Rahoton bai bayyana bayanin basussukan da sauran jihohin; Nasarawa, Niger, Filato, Yobe da Zamfara suka karba ba.

Jihohin Arewa mafi samar da harajin VAT

A wani labarin, mun ruwaito cewa jihohin Kano, Borno, Kwara, Adama da Filato ne suka fi kowace jihar Arewa samun kudaden shiga (harajin VAT) a 2024.

Hukumar tattara haraji a Najeriya (FIRS) ta fitar da sanarwar jihohin da suka samar da harajin VAT din, inda ta ce jihar Kano ta samar da jimillar Naira biliyan 4.66.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.