Sanatoci 16 daga Shiyya 1 Sun Hada Kai, Sun Goyi bayan Tinubu kan Gyaran Haraji

Sanatoci 16 daga Shiyya 1 Sun Hada Kai, Sun Goyi bayan Tinubu kan Gyaran Haraji

  • Sanatocin Kudu maso Kudu sun amince da kudirin gyaran tsarin haraji, suna cewa zai kawo ci gaba ga yankinsu da kasa baki daya
  • 'Yan majalisar dattawan sun bukaci sanatocin jihohin Arewa da ke adawa da kudirin da su guji son zuciya tare da duba bukatun kasa
  • Sun kada kuri’ar amincewa da shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio, suna masu goyon bayan jagorancinsa a majalisar kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Sanatocin yankin Kudu maso Kudu sun amince da kudirin gyaran haraji, suna masu cewa zai kawo ci gaba da daidaiton tattalin arziki.

A wata sanarwa da suka fitar a ranar Alhamis bayan taronsu a Abuja, sanatocin sun ce kudirin zai tallafa wa yankin Kudu maso Kudu da kasa baki daya.

Sanatocin shiyyar Kudu Maso Kudu sun yi magana kan muhimmancin kudurin gyaran haraji
Sanatocin Kudu maso Kudu sun goyi bayan Tinubu kan kudirin gyaran haraji. Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

Sanatoci 18 sun goyi bayan gyaran haraji

Kara karanta wannan

Kudirin Haraji: Gwamnatin Tinubu za ta rika karbar haraji a kudin gado?

Sanatocin sun roki ‘yan uwansu na Arewa da ke adawa da kudirin da su duba manufar gyaran tsarin harajin ba tare da son zuciya ba, a cewar rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan majalisar dattawan sun ce:

“Mun fahimci mahimmancin sake fasalin haraji wajen bunkasa kudaden shiga da daidaiton tattalin arziki.”

'Yan majalisar dattawan sun ce za su tabbatar an yi nazari sosai kan kudirin gyaran harajin don ya dace da bukatun al’umma musamman na Kudu maso Kudu.

Sun yi kira ga wadanda ke son kawo bambancin ra'ayi na kabilanci ko yanki a muhawara kan harajin da su guji yin hakan, "domin gudun rarrabuwar kai".

Sanatoci 16 sun amince da jagorancin Akpabio

An rahoto cewa sanatocin sun kada kuri’ar amincewa da jagorancin shugaban majalisar dattawan, Godswill Akpabio, suna masu nuna goyon baya a gare shi.

“Muna ba da cikakken goyon baya ga shugaban majalisar dattijai wajen jagorancin da zai kai ga samar da dokoki masu amfani ga kasa."

Kara karanta wannan

Dalilin da ya saka majalisa dakatar da kudirin harajin shugaba Tinubu

- A cewar sanatocin.

Wadanda suka rattaba hannu kan wannan goyon baya sun hada da sanatoci a jam’iyyun APC, PDP, da LP daga yankin Kudu maso Kudu, a cewar rahoton The Nation.

Gyaran haraji: Sanata Barau ya fuskanci bore

A wani labarin, mun ruwaito cewa nuna goyon baya ga gyaran haraji ya jawo mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I Jibrin na fuskantar bore daga Arewa.

Mazauna Arewa na zargin cewa nuna goyon baya kan kudurin sake fasalin harajin wani abu da zai cutar da su, wanda kuma zai iya kawo nakasu ga tafiyar Sanata Barau.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.