Ta Faru Ta Kare: Kotun Jigawa Ta Yankewa Miji da Mata da 'Yanuwanta 2 Hukuncin Kisa
- Wata kotu a jihar Jigawa ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan mutane hudu bisa zargin yin sihiri da kuma kisan kai
- Wadanda aka kama sun hada da miji da mata da wasu danginta, wadanda aka same su da laifin kashe Salamatu Musa a 2019
- Kotun ta saurari shaidu biyar da kuma rahoton likita, kafin ta tabbatar da hukuncin kisan kan wadanda ake zargi a wannan mako
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jigawa - Mai Shari’a Ado Yusuf Birnin-Kudu, na babban kotun Jigawa, ya yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wasu mutane hudu bisa laifin kisan kai.
Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da miji da mata, da 'yan uwan matar biyu (kani da kanwa) bisa hada baki wajen aikata kisan kan.
Ma'aurata sun yi kisan kai a Jigawa
Kotun ta same su da laifin kashe wata Salamatu Musa (mai shekaru 30), wanda suka zarga da yin sihiri a shekarar 2019, inji rahoton Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya ce miji da matar sun zargi Salamatu da yin sihirin da ya yi sanadiyyar mutuwar dansu, wanda hakan ya jawo suka lakada mata dukan mutuwa.
Wadanda aka yankewa hukuncin kisan sun hada da Hassan Isah (55), Adama Yahaya (42), Abdullahi Yahaya (35) da Maryam Daso Yahaya (28).
An ce mutanen hudu na zaune a gida daya tare da wanda suka kashe a kauyen Kwan-Dole na karamar hukumar Mallam-Madori, jihar Jigawa.
An gurfanar da ma'auratan gaban kotu
Kotun ta saurari shaidun mutane biyar, rahoton likita, da kuma bayanan da wadanda ake zargi suka bayyana a lokacin binciken 'yan sanda.
Jaridar Punch ta rahoto cewa an kama mutanen hudu da laifin hadin baki da kisan kai, laifuffukan da ke karkashin sashe na 97 da 221(b) na dokar Penal Code.
Mai shari’a Ado Birnin-Kudu ya ce wadanda ake zargin na sane da cewa akwai babban hukunci a kan abin da suka aikata, wanda ya dace da hukuncin kisa.
Kotu ta yankewa ma'auratan hukuncin kisa
Alkalin ya ce kotu ta yanke musu hukuncin shekaru shida a gidan yari kan laifin hada baki da kuma hukuncin kisa ta hanyar rataya kan laifin kisan kai.
Duk da haka, kotun ta ba ma'auratan da 'yan uwan matar biyu damar daukaka kara cikin kwanaki 90 daga lokacin da aka yanke musu hukuncin.
Wannan hukunci ya nuna mahimmancin doka wajen yaki da kisan kai da tsananta wa mutane bisa zarge-zargen da ba su da tushe ko asali.
Kotu ta yankewa 'yan fashi hukuncin kisa
A wani labarin, mun ruwaito cewa babbar kotun jihar Kwara, karkashin Mai shari’a Haleemah Salman ta yanke hukuncin kisa ga wasu mutane biyar kan fashin bankin Offa.
Kotun ta samu wadanda ake zargin da aikata laifuffukan da suka shafi fashi da makami, kashe 'yan sanda da farar hula da kumamallakar bindigogi a cikin Afrilun 2018.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng