Matasan N Power na Jiran Bashinsu, Gobara Ta Laƙume Ma'ajiyar NSIPA, Kaya Sun Kone

Matasan N Power na Jiran Bashinsu, Gobara Ta Laƙume Ma'ajiyar NSIPA, Kaya Sun Kone

  • Gobara ta kama a wurin adana kaya na hukumar NSIPA da ke karkashin ma'aikatar jin kai da walwala a birnin Tarayya Abuja
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa gobarar ta yi sanadin lalacewar abubuwa masu amfani a ofishin ciki har da kayan masu muhimmanci
  • An tabbatar da cewa gobarar ta lakume kayan horaswa da aka ware saboda matasan N-Power yayin da suke kiran a biya su kudinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - An shiga cikin tashin hankali yayin da gobara ta kama a wurin adana kaya na hukumar NSIPA da ke Abuja.

Gobarar ta lakume abubuwa masu amfani ciki har da kayan horaswa na matasan N-Power karkashin hukumar NSIPA.

Gobara ta kama a ofishin hukumar NSIPA a Abuja
An tafka asara bayan gobara ta lakume kayayyaki a ofishin hukumar NSIPA. Hoto: Yutyilda Nentawe
Asali: Twitter

Gobara ta kama a ofishin hukumar NSIPA

Karamin Ministan jin kai da walwala, Dr. Yusuf Sununu ya kaddamar da kwamitin bincike kan lamarin, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

TCN zai magance matsalolin wutar lantarki, an fara inganta manyan tashoshi 3

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr. Sununu yayin ziyara wurin da lamarin ya faru, ya sha alwashin kawo tsare-tsare da za su kare faruwar hakan a gaba.

Ministan duk da haka ya ce za su fara ba masu cin gajiyar horaswa saboda yin amfani da kayayyakin da aka siya.

Minista ya kafa kwamitin bincike kan lamarin

"Kwamitin zai yi bincike domin gano yawan kayan da aka yi asara, kuma za mu tabbatar da daukar matakai domin kare faruwar hakan a gaba."
"Nan ba da jimawa ba za mu fara ba masu cin gajiyar horaswa saboda amfani da kayan da aka riga aka samar."

- Yusuf Sununu

Dr Sununu ya yabawa jami'an hukumar kashe gobara da rundunar yan sanda kan gudunmawar da suka bayar.

Legit Hausa ta tattauna da wani matashi dan N-Power

Wani wanda ya ci gajiyar N-Power a Gombe ya yi tsokaci kan wanann iftila'i da ya faru a ofishin hukumar NSIPA.

Kara karanta wannan

Jami'in gwamnati ya yi tone tone, ya fallasa yadda tsohon gwamna ya wawure N5bn

Musa Abubakar wanda na daya daga cikin masu bin basukan watanni ya yi zargin da gangan aka tayar da wutar.

"Akwai zargin wutar kunna ta aka yi saboda yin rufa-rufa kan badakalar da aka yi."
"A daidai lokacin da ake kokarin biyan basukan N-Power da kuma wa'adi da Majalisa ta ba Tinubu wutar ta tashi dole za a yi wani abu."

- Musa Abubakar

NSIPA: Majalisar tarayya ta ba Tinubu wa'adi

Kun ji cewa Majalisar wakilai ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin buɗe asusun hukumar NSIPA daga nan zuwa sa'o'i 72 masu zuwa.

Majalisar ta ɗauki wannan matakin ne bayan amincewa da kudirin da mataimakin kakakin majalisa, Benjamin Kalu da yan majalisa 20 suka gabatar.

Hon. Kalu ya shaidawa majalisa yayin gabatar da kudirin cewa hukumar na taimakawa wajen yaƙar fatara da tallafawa matasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.