Sojoji Sun Yi Ruwan Bama Bamai kan Ƴan Bindiga a Arewa, An Kashe Miyagu Masu yawa

Sojoji Sun Yi Ruwan Bama Bamai kan Ƴan Bindiga a Arewa, An Kashe Miyagu Masu yawa

  • Rundunar sojin sama ta yi ruwan bama bamai kan sansanin 'yan bindiga a jihar Zamfara, inda aka hallaka 'yan ta'adda da dama
  • Wata majiya ta shaida cewa harin sojojin saman ya biyo bayan bayanan sirri kan shirin hare-hare da 'yan ta'addan ke yi a jihar
  • Jami'an tsaro sun bukaci haɗin kai daga mazauna Zamfara yayin da aka tabbatar da nasarar lalata sansanonin 'yan ta'addan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Rundunar sojin saman Najeriya ta yi ruwan bama bamai kan mafakar 'yan ta'adda a Rugan Mai Taru, Arewacin ƙaramar hukumar Tsafe, jihar Zamfara.

Ruwan bama bamai da jiragen sojin suka yi a safiyar Laraba ya hallaka 'yan ta'adda da dama tare da lalata kayayyakin tsaro a sansaninsu.

Sojoji sun nemi hadin kan jama'a yayin da suka samu nasarar tarwatsa sansanin 'yan bindigar Zamfara
Zamfara: Sojojin saman Najeriya sun tarwatsa sansanin 'yan bindiga, sun hallaka miyagu. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Zagazola Makama, wani mai sharhi kan lamuran tsaro a Arewa maso Kudu da kuma Tafkin Chadi ne ya fitar da rahoton a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Barau ya bukaci majalisa ta mayar da sunan Yusuf Maitama a jami'ar FUE

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun yi ruwan bama bamai a Zamfara

Rahoton Makama ya bayyana cewa harin, mai suna 'Fansan Yanma', ya biyo bayan bayanan sirri da sojojin suka samu kan 'yan ta'addan da ke shirin kai hare-hare.

Binciken farko na sojojin ya nuna cewa harin ya lalata ginin sansanin 'yan ta'addan da kuma tarwatsa shirin kai hare-haren da suka yi.

Mazauna garuruwan da ke kusa sun ce sun ji fashewar bama-bamai tare da ganin hayaƙi mai yawa yana tashi daga sansanin 'yan bindigar.

Jami'an tsaro sun nemi hadin kan jama'a

Rahoton Makama ya ce wannan hari na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na karya lagon 'yan ta'adda da ke barazana ga zaman lafiya a Arewacin kasar.

Rundunar soji ta ce za ta ci gaba da kai hare-haren sama don tabbatar da tsaro a yankunan da ke fama da rikicin tsaro musamman a Arewa maso Yamma.

Ma'aikatan tsaro sun yi kira ga mazauna yankin da su bayar da haɗin kai wajen ba da bayanan sirri domin cigaba da samun irin wannan nasarar.

Kara karanta wannan

Sultan da shugaban CAN sun ajiye bambancin addini, sun mika bukata 1 ga Tinubu

Sojoji sun sheke 'yan bindiga a Zamfara

A wani labarin, mun ruwaito cewa sojojin saman Najeriya sun halaka miyagun 'yan bindiga masu yawa a Babban Kauye da ke ƙaramar hukumar Tsafe, jihar Zamfara.

Daraktan hulɗa da jama'a da yaɗa labarai na rundunar NAF, Olusola Akinboyewa, wanda ya bayyana hakan ya sanar da cewa hare haren sun yi nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.