'Majalisa Ta Fi Karfin a Yi Mata Barazana': Akpabio Ya Ja Kunne kan Kudirin Haraji
- Bayan yada jita-jitar cewa Majalisa ta dakatar da tattaunawa kan kudirin haraji, Godswill Akpabio ya yi magana
- Shugaban Majalisar ya ce babu wanda ya isa ya tilasta su dakatar da abin da suke ganin zai taimaki al'ummar Najeriya
- Hakan ya biyo bayan yada rade-radin cewa Majalisar da dakatar da tattaunawa kan kudirin saboda ce-ce-ku-ce da ake yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya yi magana kan sabon kudirin haraji a Najeriya.
Akpabio ya ce babu maganar dakatar da tattaunawa kan kudirin haraji kamar yadda wasu ke yaɗawa.
Godswill Akpabio ya magantu kan sabon kudirin haraji
Shugaban Majalisar ya fadi haka ne a yau Alhamis 5 ga watan Disambar 2024 yayin zamansu a birnin Abuja, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akpabio ya ce babu abin da zai hana aiwatar da kudirin inda ya ce kullum burinsu kare muradun yan kasa ne.
Har ila yau, Akpabio ya ce babu wani abu ko wasu mutane daga waje da za su tsoratar da su kan gudanar da abin da suka sanya a gaba.
Akpabio ya ce kudirin zai taimaki yan Najeriya
Shugaban Majalisar ya fadi haka ne yayin martani ga wasu rahotanni cewa an dakatar da tattaunawa kan kudirin harajin bayan ce-ce-ku-ce a kai.
"Babu wanda ya isa saka mu a gaba kan abin da muke ganin zai taimaki yan Najeriya, wannan kudiri na dauke da abubuwa da zai taimaki al'umma."
- Godswill Akpabio
A bangarensa, shugaban masu rinjaye a Majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele ya ce bai kamata mutane su yi ta yada labaran karya ba.
Akpabio ya yi barazana ga wasu sanatoci
Kun ji cewa yayin zaman Majalisar Dattawa a ranar Talata 3 ga watan Disambar 2024, shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya gargadi wasu sanatoci.
Akpabio ya sha alwashin tube duk wani shugaban kwamiti da ya gaza yin abin da ake tsammani daga gare shi a Majalisar Dattawan kasar.
Hakan na zuwa ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan sabon kudirin haraji da wasu ke zargin zai yi rugu-rugu da tattalin arzikin wasu yankuna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng