Tsohon 'Dan Takarar Gwamna a PDP, Sanata Dino Melaye Ya Yi Babban Rashi

Tsohon 'Dan Takarar Gwamna a PDP, Sanata Dino Melaye Ya Yi Babban Rashi

  • Tsohon dan takarar gwamna a jihar Kogi karkashin jam'iyyar PDP, Dino Melaye ya sanar da rasuwar surukarsa
  • Melaye ya tabbatar da mutuwar matar kaninsa Timothy Melaye a yau Alhamis 5 ga watan Disambar 2024
  • Marigayiyar mai suna Damilola Melaye ta rasu ne a jiya Laraba 4 ga watan Disambar 2024 a Lagos bayan fama da jinya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Sanata Dino Melaye ya sanar da babban rashin da suka yi na daya daga cikin iyalansu a jihar Lagos.

Melaye ya tabbatar da rasuwar matar dan uwansa, Timothy Melaye mai suna Damilola Melaye bayan fama da jinya.

Sanata Dino Melaye ya yi rashin surukarsa
Tsohon dan takarar gwamna a PDP, Dino Melaye ya sanar da rasuwar surukarsa. Hoto: Dino Melaye.
Asali: Facebook

Sanata Dino Melaye ya bukaci addu'o'in 'yan Najeriya

Sanatan a bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Alhamis 5 ga watan Disambar 2024.

Kara karanta wannan

Sanata Barau: Matasan Arewa sun yi gangami a Abuja, sun goyi bayan gyaran haraji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, Melaye ya ce marigayiyar ta rasu ne a jiya Laraba 4 ga watan Disambar 2024 a Lagos.

Melaye ya bukaci addu'o'in al'umma kan rashin da suka yi yayin da suke cikin alhinin mutuwar matar.

Dino Melaye ya sanar da rasuwar surukarsa a Lagos

"Cikin alhini da mika lamura ga Ubangiji, iyalan Melaye na sanar da rasuwar yarmu kuma suruka wacce ta kasance mata ga Timothy Melaye."
"Marigayiyar ta rasu ne a jiya Laraba 4 ga watan Disambar 2024 a jihar Lagos bayan fama da jinya."
"Muna neman addu'o'inku yayin da muke cigaba da alhini, Ubangiji ya yi muku albarka baki dayanku."

- Dino Melaye

Jam'iyyar PDP ta dakatar da Dino Melaye

Kun ji cewa jam'iyyar adawa ta PDP a Kogi ta dakatar da tsohon dan takarar gwamnanta na zaben 2023 a jihar, Sanata Dino Melaye.

An ruwaito cewa jam'iyyar PDP ta dakatar da Melaye ne bisa zargin ya aikata laifuffukan da suka saba da'a da cin mutuncin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Kwanaki da aurenta, yar Kwankwaso ta saka mahaifinta alfahari, Aisha ta sha yabo

Ga dukkan alamu dai kalamansa na baya-bayan nan sun yi illa ga muradu da hadin kan PDP, wanda ya sa aka dakatar da shi daga jam'iyyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.